KAI TSAYE: An tashi wasa, Nigeria 0-0 Sierra Leone (Wasan kwallon fidda gwanin gasar AFCON)
Najeriya tana gwarawa da kasar Sierra Leone a wasar kwallon fidda gwanin gasar kasashen nahiyar Afrika da za'ayi a 2022.
Yan kwallon Super Eagles ne kan gaba da maki 7 a zaurensu bayan nasara kan Lesotho, Benin da kuma kunnen jaki da Sierra Leone.
Najeriya ta tashi 4-4 da Sierra Leone a wasar da aka buga a filin kwallon Sam Ogbemudia dake Benin City, jihar Edo ranar Juma'a.
Yanzu yan kwallon Super Eagles sun garzaya birnin Freetown, kasar Siera Leone domin buga wasa na biyu.

Asali: Getty Images
An tashi wasa Nigeria 0-0 Sierra Leone
An tashi wasan Najeriya da Sierra Leone babu wanda ya zura kwallo ko guda.