'Yar hidimar kasa ta haihu a sansanin bautar kasa da ke Ekiti

'Yar hidimar kasa ta haihu a sansanin bautar kasa da ke Ekiti

- Wata mata ta haifi jaririya a sansanin 'yan bautar kasa na jihar Ekiti a ranar Litinin

- Matar ta kamu da nakuda ne a sansanin, inda aka kai ta babban asibiti ta haihu

- Yanzu haka, matar da jaririyarta suna cikin koshin lafiya, cewar kakakin sansanin

Wata mata ta haihu a sansanin 'yan bautar kasa na jihar Ekiti, inda ta haifi santaleliyar jaririya, jaridar The Cable ta wallafa.

Matar tana daya daga cikin masu bautar kasa 653 da aka tura jihar Ekiti na shekarar 2020 a halin yanzu.

Kamar yadda NAN ta ruwaito, Rose Onoja, Kakakin sansanin ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin.

A cewar Onoja, sai da aka garzaya da matar asibitin cikin sansanin lokacin da ta fara nakuda.

"Daga asibitin, an mayar da ita Babban asibitin Emure, inda ta haifi jaririya. Yanzu haka matar da jaririyarta suna cikin koshin lafiya," a cewarta.

Al'amarin ya faru ne tun bayan NYSC ta samar da kotu, wacce take ladabtar da duk wanda ya karya doka.

KU KARANTA: Ndume: Buhari na zagaye da manyan barayi a mulkinsa

'Yar hidimar kasa ta haihu a sansanin bautar kasa da ke Ekiti
'Yar hidimar kasa ta haihu a sansanin bautar kasa da ke Ekiti. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugabancin kasa a 2023: PDP na fuskantar babban kalubale a kudu maso gabas

A wani labari na daban, Gwamnatin jihar Kaduna tace wata Rundunar Operation Thunder Strike ta samu nasarar ceto wasu mutane 9 da masu garkuwa da mutane suka sace a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadi da rana.

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da hakan ne ta wata takarda, wacce ta fito daga wurin Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida.

Kamar yadda takardar ta zo: "Rundunar Operation Thunder Strike ta fita sintiri wuraren Akilubu- Gidan Busa a hanyar Kaduna zuwa Abuja, bayan an sanar da su cewa wasu 'yan bindiga sun dakatar da babban titi, da misalin karfe 4."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng