Babban abun alheri da ya taba samun Najeriya shine PDP, Atiku

Babban abun alheri da ya taba samun Najeriya shine PDP, Atiku

- Najeriya ba ta da babban abokin da ya wuce Jam'iyyar PDP, cewar Atiku Abubakar

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fadi hakan ne a Twitter

- Ya ce PDP ce kadai jam'iyyar da za ta iya yi wa kowa adalci a Najeriya

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya ce PDP ce babban abokin Najeriya.

Atiku ya ce PDP ta mulki Najeriya na tsawon shekaru 16 kafin APC ta amshi mulkin Najeriya a 2015, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Atiku ya wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Twitter, inda yace, "PDP ce babban abokin Najeriya. Duk bangarorin Najeriya suna bukatar jam'iyyar da za ta gyara Najeriya, ba wacce za ta lalata ta ba.

"Jam'iyyar PDP ta tabbatar da za ta gyara Najeriya, sannan ina rokon 'yan Najeriya da su amince da jam'iyyar don za ta tabbatar da adalci ga kowa."

KU KARANTA: Yadda rikicin Rahama Sadau ya janyo rikicin cikin gida da rabewar kai a Kannywood

Babban abun alheri da ya taba samun Najeriya shine PDP, Atiku
Babban abun alheri da ya taba samun Najeriya shine PDP, Atiku. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotunan tamfatsetsen gidan da Emmanuella ta gina wa mahaifiyarta

A wani labari na daban, Ali Ndume, sanata mai wakiltar kudancin Borno, ya ce da yawa daga cikin wadanda suke karkasin shugaban kasa Muhammadu Buhari barayi ne.

A ranar Lahadi, gidan talabijin din Channels sun yi hira da sanatan inda ya sanar da hakan, ya ce akwai mutanen da suke kokarin ganin bayan cigaba a mulkinsa.

Bayan an tambayeshi a kan yadda mulkin APC yake tafiya, cewa yayi gaskiya ba ya farinciki da tafiyar ta shekaru 5. Duk da suna yin iyakar kokarinsu, amma akwai gurabe da dama da ya kamata a cike.

A cewarsa, duk da kokarinsu, sai mutane sun zagesu, jaridar The Cable ta wallafa.

Ya ce shugaba Buhari sai dai ya bayar da umarni, amma ba zai iya zuwa yayi ayyuka da kansa ba, don haka mafi yawan matsalolin daga masu yin ayyukan ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel