Yadda jami'an SARS ci zarafina tare da watsa min barkonon tsohuwa, Gwamnan APC

Yadda jami'an SARS ci zarafina tare da watsa min barkonon tsohuwa, Gwamnan APC

- Ni kaina na fuskanci cutarwa a hannun 'yan sanda a 2014, cewar gwamnan jihar Ekiti, Dr Fayemi Kayode

- A cewarsa, lokacin da suke yakin neman zabe, saboda tsananin cutarwa, daya daga cikin jiga-jigan APC, Taiwo Akinsola, ya rasu

- Kayode ya ce zai cigaba da mara wa matasan jiharsa masu kyawun niyya baya, don dakatar da zaluncin 'yan sanda

A Jiya ne gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi ya bayar da labarin irin bakar wahalar da ya fuskanta a hannun 'yan sanda, inda yace yana daga cikin wadanda 'yan sanda suka cutar a 2014.

Gwamnan ya ce wasu daga cikin 'yan sandan, sun taimaka masa kwarai, a cewarsa, wasu 'yan sanda sun jefa masa barkonon tsohuwa yayin yakin neman zaben takarar gwamnan jihar a 2014.

KU KARANTA: Tabbas na yi lalata da jikata, amma ban san ta samu ciki ba, tsoho mai shekaru 70

Bayan 'yan jam'iyyar PDP sun gama rali, jam'iyyar APC ma ta fara nata, inda Fayemi da masu mara masa baya su ka bi titina suna shara, kawai sai rundunar 'yan sanda ta afka musu,.Garin hakan har wani shugaban APC, Taiwo Akinsola, ya rasa ransa.

Yadda jami'an SARS suka kusa halaka ni, Gwamnan APC
Yadda jami'an SARS suka kusa halaka ni, Gwamnan APC. Hoto daga @Thisday
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dan dagacin kauye ya mutu bayan arangamar jami'an kwastam da 'yan sumogal

Gwamnan ya fadi hakan ne a wata hira da aka yi da masu fadi a ji a kan zanga-zangar EndSARS wacce ta karade kasar, inda Fayemi yace zai cigaba da yin kira a kan dakatar da mugayen 'yan sanda, shi da masu kyakkyawar niyya a cikin masu zanga-zangar.

Ya ce muguntar da 'yan sanda suke yi tana daya daga cikin manyan matsalolin da al'umma take fuskanta, ThisDay ta wallafa.

Yace a jihar Ekiti, sun yi na'am da zanga-zangar, saboda kyakkyawan makasudin ta. Matasan jihar Ekiti sun yi zanga-zangar da kyakkyawar niyya kuma cikin lumana. A cewarsa a karo na farko kenan da majalisar zartarwa tayi gaggawar amsar korafi.

A wani labari na daban, Akwai mata da yawa masu karfin hali, wadanda suke gogayya da mazaje a ma'aikatu daban-daban.

Kuma sun zama kallabi tsakanin rawuna, ta yadda ko mazan basu isa su wuce da saninsu ba. Tracey ta kai shekaru 3 tana tukin babbar mota. Sai gashi ta yi korafi a kan yadda take fuskantar suka da kushe daga abokan aikinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel