Hotunan tamfatsetsen gidan da Emmanuella ta gina wa mahaifiyarta
- Wannan yarinyar mai wasannin ban dariya, Emmanuella ta canja wa mahaifiyarta rayuwa
- Yarinyar ta maka wa mahaifiyarta katafaren gida, na gani da fadi sannan ta cika shi da kayan alatu
- Duk wanda ya kalli hotunan gidan, dole ya amince da cewa aljannar duniya ne gidan
Karamar yarinyar nan, wacce tayi shuhura a wasannin ban dariya, Emmanuella, ta saka mahaifiyarta cikin matsanancin farinciki.
Yarinyar, mai shekaru 10 da haihuwa ta gina wa mahaifiyarta katafaren gida don nuna mata dadin da taji a kan yadda ta tsaya mata kuma ta dage wurin ganin ta riki aikinta yadda ya kamata.
KU KARANTA: FG ta shiga matukar damuwa a kan barkewar cutar zazzabin Lassa
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarta, babban burin mahaifiyarta shine ta mallaki gida mai ban sha'awa, shiyasa tayi iyakar kokarinta wurin cika mata burinta.
A cewar Emmanuella, ta yi alkawarin canja mata wani katafaren, wanda yafi wannan, nan da shekarar 2021.
KU KARANTA: Shugaban karamar hukuma ya lallasa wa mai neman kujerarsa mugun duka
Kamar yadda Emmanuella ta wallafa, ta ginawa mahaifiyarta gidan ne, sakamakon addu'a da kuma cikakken kwarin guiwa da take bata, har ta kai wannan matakin.
Yanzu haka tana ginin wani katafaren gidan, kuma za ta karasa shi nan da shekara mai zuwa. Ta bayyana yadda take matukar kaunar mahaifiyarta.
A wani labari na daban, jarumar finafinan Yarabawa, Sandra Alhassan, ta bayyana irin saurayin da zata iya kulawa, da wanda ko kallo bai isheta ba, jaridar Vanguard ta wallafa.
Jarumar, wacce mahaifiyarta asalin 'yar jihar Edo ce, mahaifinta kuma dan jihar Kano, ta ce ta ki jinin kazamin saurayi.
Kyakkyawar, dirarriyar jarumar ta ce tana matukar son kula samari masu kyau, tsafta, aji da kuma dukiya. Yayin da ta tsani munana, talakawa da kuma kazaman samari.
Kamar yadda ta wallafa: "Ba zan iya sauraron kazamai, gajoji da kuma talakawan samari ba. Sannan na tsani ganin saurayi mai cike da yarinta"
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng