Shugaban karamar hukuma ya lallasa wa mai neman kujerarsa mugun duka
- Ana cewa siyasa rigar 'yanci, amma a jihar Kano kuwa, al'amarin ya sauya salo, ya koma yaki
- Shugaban karamar hukumar Gaya, yayi wa mai neman kujerarsa dukan kawo wuka
- Kamar yadda dan uwansa ya tabbatar, an yi masa dukan har sai da ya fita hayyacinsa ya suma
Ana zargin shugaban karamar hukumar Gaya da ke jihar Kano, Ahmad Abdullahi Tashi, da Shu'aibu Gamarya, shugaban majalisar kansilolinsa, da yi wa mai neman kujerarsa, Hafizu Sunusi Mahmoud Gaya, dukan tsiya.
Al'amarin ya faru ne daidai lokacin da 'yan siyasan suke fafutukar ganin sun samu nasarar cin zaben da za'ayi na kananan Hukumomi a watan Janairun 2021.
Wani dan uwan dan takarar da ya sha bugu, Uwaisu Sunusi Mahmoud Gaya, wanda ganau ne shi ba jiyau ya ce, "Sun hau shi da duka har sai da ya suma, ya kuma daina magana, bayan ya farka daga sumar suka dasa daga inda suka tsaya".
Ya sanar da jaridar Aminiya cewa al'amarin ya faru ne da misalin karfe 2 na ranar Laraba, a gaban 'yan kwamitin sasanci tsakanin 'yan takarar, wanda Gwamna Abdullahi Ganduje ya kafa.
Dama ya kafa kwamitin ne don yin sulhu da sasanci tsakanin 'yan takara yayin zaben fid da gwani da za a yi a jihar.
A cewar Uwaisu, "Mun ba su sarari ne a bisa umarnin shugaban karamar hukumar, wanda yace duk wadanda suka rako dan takara su koma gefe su ba su sarari don a yi sasanci. Kawai shugaban karamar hukumar ya tashi da Gamarya suka hau dukan dan takarar shugabancin karamar hukumar Gaya.
"Sun koma dukan Hafizu har sai da suka ga ya kasa tashi, ya suma. Da kyar muka samu muka cece sa daga hannunsu, muka kai shi asibitin Gaya."
"Daga bisani Sanatan Kano ta kudu, Kabiru Gaya ya bayar da umarnin a mayar dashi asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, don ya samu cikakkiyar kukawa," inji Uwaisu.
KU KARANTA: Ni ne sabuwar ma'anar damokaradiyya, Obaseki yayin da yake daukar rantsuwa
KU KARANTA: Saraki ya umarci biyan wani hadimarsa N100m duk wata yayin da yake gwamna, Tsohon akawun Kwara
A wani labari na daban, Murtala Gwarmai, mai ba wa gwamnan jihar Kano shawara a kan harkokin matasa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya rarraba wa matasa jakuna a ranar Alhamis.
Gwarmai, ya gwangwaje matasan da jakuna, babura da kekunan hawa da sauran su, Daily Trust ta wallafa. Kamar yadda rahotonni suka kammala, matasa a kalla 40 ne suka sha daga romon damokaradiyyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng