Bidiyon mace mai sana'ar jan babbar mota ya janyo cece-kuce
- Wata direbar babbar mota, mai karancin shekaru, Tracey, tana shan gwagwarmayar tare da direbobi maza
- Duk da jajircewarta, tana fuskantar kalubale iri-iri, tsakaninta 'yan uwan aikinta a matsayinta na 'ya mace
- Tracey, ta nemi shawarar yadda za ta magance matsalar yadda abokan aikinta suke caccakar ta suna kushe ta
Akwai mata da yawa masu karfin hali, wadanda suke gogayya da mazaje a ma'aikatu daban-daban. Kuma sun zama kallabi tsakanin rawuna, ta yadda ko mazan basu isa su wuce da saninsu ba.
Tracey ta kai shekaru 3 tana tukin babbar mota. Sai gashi ta yi korafi a kan yadda take fuskantar suka da kushe daga abokan aikinta.
Akwai lokutan da ake tambayarta idan kawai ta fita yawon shakatawa ne ko kuma aiki.
Akwai lokutan da maza suke caccakarta da bakaken maganganu, idan suka hango cewa mace ce take tukin babbar mota.
Matar mai diya mace 1, tana bukatar yadda za ta shawo kan wannan matsalar.
Bayan tayi wallafar ne wani Steve Harvey, babban mai shirya finafinan Amurika, yace ta cigaba da aikinta. Kada ta taba damuwa da maganar mutane, saboda aikinta mai tsafta ne.
Wani China Dunn cewa yayi, "Na kai shekara 40 ina tukin mota, na kai mutane wurare daban daban. Matsawar kina son aikinki, kada ki kuskura makiya su kashe miki jiki."
KU KARANTA: Mummuna, kazami kuma talakan namiji yana bata min rai - Jarumar fim
KU KARANTA: Shugaban karamar hukuma ya lallasa wa mai neman kujerarsa mugun duka
A wani labari na daban, dan dagacin wani kauye ya rasa ransa sakamakon rikicin jami'an kwastam da wasu matasa 'yan sumogal a jihar Kebbi., jaridar The Punch ta wallafa.
Rikicin ya hargitse tsakanin jami'an kwastam na Kaduna da suke aiki a jihar Kebbi, da wasu matasa, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar wani saurayi.
Kamar yadda rahotonni suka kammala, wanda aka kashe, Abdul-Rahman Sani, da ne ga dagacin kauyen Budi, Alhaji Sani Muhammad, na karamar hukumar Bunza.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng