Yadda rikicin Rahama Sadau ya janyo rikicin cikin gida da rabewar kai a Kannywood

Yadda rikicin Rahama Sadau ya janyo rikicin cikin gida da rabewar kai a Kannywood

- Mako biyu kenan da Rahma Sadau ta saki hotunanta, wadanda suka janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani

- Har yanzu hotunan suna cigaba da janyo maganganu, har da musayar yawu tsakanin jarumai daban-daban na Kannywood

- Hotunan sun janyo rabuwar kawunan jarumai, inda wasu suka koma bayan Rahama, wasu kuma suka koma sukarta

Kamar yadda rahotonni suka kammala, jaruma Hafsat Shehu wacce tayi aure babu jimawa kuma auren ya mutu da kuma jaruma Mansura Isah sun yi musayar yawu.

Bayan caccakar juna da suka yi, Mansura Isah ta yi gaggawar goge tsokacin da tayi, inda kafafen sada zumunta suka dauki zafi, Daily Trust ta wallafa.

Mansurah tayi amfani da shafinta na Instagram inda tace da bata so yin magana ba, amma kowa yana zunubi. Kuma kowa yana da kashi a gindinsa.

Ya kamata a dakata da caccakar Sadau haka, duk masu caccakarta sanye da hijabai duk na munafurci ne, suna yaudarar mutane. Su ji tsoron Allah, kuma su duba abubuwan da suka aikata a baya.

Bayan ganin wannan wallafar ta Mansurah, Hafsat Shehu tayi tsokaci a kasan wallafar, inda tace "Mun san matan aure masu bin maza, kuma kowa yana zunubi, kowa yana da nashi guntun kashin."

Tsohuwar jaruma Fati Slow kuma ta yi bidiyo, inda tace kada a bari su fara sakin bama-bamai a kan matan Yarabawa. Matsawar Mansura ta sake magana, za su "tona mata asiri."

Jaruma Rashida mai sa'a ta ce wannan sa-in-sa da 'yan Kannywood suke yi alama ce da take nuna cewa kan duk jaruman Kannywood a rabe yake.

KU KARANTA: FG ta shiga matukar damuwa a kan barkewar cutar zazzabin Lassa

Yadda rikicin Rahama Sadau ya janyo rikicin cikin gida da rabewar kai a Kannywood
Yadda rikicin Rahama Sadau ya janyo rikicin cikin gida da rabewar kai a Kannywood. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Romon damokaradiyya: Hadimin Ganduje ya gwangwaje jama'a da tattalin Jakuna

A wani labari na daban, ana zargin shugaban karamar hukumar Gaya da ke jihar Kano, Ahmad Abdullahi Tashi, da Shu'aibu Gamarya, shugaban majalisar kansilolinsa, da yi wa mai neman kujerarsa, Hafizu Sunusi Mahmoud Gaya, dukan tsiya.

Al'amarin ya faru ne daidai lokacin da 'yan siyasan suke fafutukar ganin sun samu nasarar cin zaben da za'ayi na kananan Hukumomi a watan Janairun 2021.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng