Karya ne, gwamnatin Buhari ba ta shirin biyan tubabbun yan Boko Haram N150,000 a wata, Bashir Ahmad

Karya ne, gwamnatin Buhari ba ta shirin biyan tubabbun yan Boko Haram N150,000 a wata, Bashir Ahmad

Hadimin shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya karyata maganar cewa gwamnatin Buhari na shirin fara biyan tubabbun yan Boko Haram N150,000 a wata.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Najeriya na biyan tubabbun yan Boko Haram albashi N150,000 a wata.

Amma Bashir Ahmad yace wannan labarin bogi ne kuma ya yi kira ga yan Najerita suyi watsi da hakan.

Ahmad ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Yace: "Gwamnatin tarayya ba ta shirin fara biyan tubabbun yan Boko Haram kudi N150,000 a wata."

"Labari ne maras asali kuma na bogi."

Karya ne, gwamnatin Buhari ba ta shirin biyan tubabbun yan Boko Haram N150,000 a wata, Bashir Ahmad
Tubabbun yan Boko Haram Hoto: UGC
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel