Yanzu-yanzu: Shahrarren tsohon shugaban kasan Ghana, Jerry Rawlings ya mutu
- Jerry Rawlings wanda aka fi sani da Papa J ya kwanta dama
- Tsohon shugaban ya mutu ne da safiyar Alhamis a cikin kasarsa
- Ya jagoranci kasar a matsayin Soja kuma a matsayin farin hula
Shahrarren tsohon shugaban kasar Ghana, Jerry Rawlings, ya mutu bayan kamuwa da cutar COVID-19.
TheCable ta tattaro cewa tsohon shugaban kasan ya mutu ne a asibitin Korle-Bu dake Accra, babbar birnin kasar, da safiya Alhamis.
Rawlings, wanda tsohon shugaban mulkin Soja ne ya yi mulkin Ghana tsakanin 1981 da 2001.
Ya kasance shugaban kasa karkashin mulkin Soja zuwa 1992, sannan ya koma demokradiyya kuma yayi mulki zuwa 2001.
A matsayinsa na hafsa a hukumar Sojin saman Ghana, Rawlings yayi kokarin juyin mulki a Mayun 15, 1979, amma bai samu nasara ba.
KU KARANTA: Mun amince da komawar Gwamna Ebonyi APC, PDP ba tayi mana halacci ba - Ohanaeze Ndigbo

Asali: UGC
Jiya mun kawo muku cewa Firam Ministan kasar Bahrain, Sheikh Khalifa bin Salman al Khalifa, ya mutu, sanarwa daga fadar mulki.
Sheikh Khalifa bin Salman al Khalifa ya rasu yana mai shekaru 84 a duniya.
Firam Ministan ya mutu ne da safiyar Laraba a asibitin Mayo Clinic dake Amurka, kamfanin dillancin labaran Bahrain ya ruwaito.
KU KARANTA: Bayan tashin Bam na jiya a Saudiyya, an kai hari ofishin jakadancin kasar dake Hague
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng