Duba gidan Kobe Bryant da ke Pennsylvania da aka siya a $810,000

Duba gidan Kobe Bryant da ke Pennsylvania da aka siya a $810,000

- An sayar da gidan da Kobe Bryant ya taso da ke Pennsylvania dala 810,000

- Kobe Bryant mashahurin dan wasan kwallon kwando ne kafin rasuwarsa a Janairun 2020

- Labarai sun yi ta yaduwa a kan sayar da gidan Bryant da aka yi

Labarai sun yi ta yawo a kan sayar da gidan Kobe Bryant da aka yi na Pennsylvania, watanni 10 da mutuwar mashahurin dan wasan kwallon ragar sakamakon hatsarin jirgin sama.

A gidan ne Bryant yake yin kwallon a lokacin da yake da rai. Kamar yadda TMZ suka ruwaito, an sayar da gidan dala 810,000 wanda zai kai Naira miliyan 307.8.

TMZ sun kara da cewa gidan yana da dakunan kwana guda 5, kuma Kobe ya ji dadin rayuwarsa a gidan tun yana da karancin shekaru.

Duba gidan Kobe Bryant da ke Pennsylvania da aka siya a $810,000
Duba gidan Kobe Bryant da ke Pennsylvania da aka siya a $810,000. Hoto daga Allen Berezovsky
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Kotu ta bukaci a tsare dalibin da yayi wa mahaifiyarsa mugun duka

'Yan uwan Kobe Bryant sun zauna a gidan na tsawon lokaci, sai da 2008 tayi, suka koma wani gidan na gani da fadi a Los Angeles.

Duk da dai har yanzu ba a sanar da sunan wanda ya siya gidan ba, amma tabbas zai ji dadin yin wasan kwallon raga a gidan saboda akwai kayan horo.

An haifi Kobe Bryant a ranar 23 ga watan Augusta 1978, sannan ya rasu a ranar 26 ga watan Janairun 2020 sakamakon hatsarin jirgin sama wanda yayi ajalin diyarsa Gianna.

Ya yi rayuwarsa a Los Angeles sannan ya samu jinjina da yaba wa iri-iri kafin ya daina wasan kwallon.

KU KARANTA: Ina dakile kawance matukar kawa ta wuce wata 6 babu mashinshini - Matar aure

A wani labari na daban, wacce aka yi wa fyade ta ki bayar da shaida a kotu a kan wanda yayi mata fyade, a cewarta, ya gamsar da ita kwarai.

Kamar yadda New Zimbabwe suka ruwaito, mamaki ya kama wani alkali a wata kotun majistare da ke Botswana, yayin da wata wacce Oscar Chabaya mai shekaru 34 ya yiwa fyade ta ki bayar da shaida a kansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng