A gida na haifa 'ya'ya 13 ba tare da zuwa asibiti ba, mahaifiyar yara 15

A gida na haifa 'ya'ya 13 ba tare da zuwa asibiti ba, mahaifiyar yara 15

- Hussaina Salisu ta ce ta haifi 13 daga cikin yaranta 15 a gida

- Salisu ta ce bata fuskantar wahalhalu yayin haihuwa

- Matar mai shekaru 54 ta shawarci mata, kada su kuskura su yi irin haka

Hussaina Salisu, 'yar karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna, ta ce cikin yaranta 15, ta haifi guda 13 ita kadai a gida. Ta ce bata taba fuskantar wasu wahalhalu ba yayin haihuwar yaranta ba.

A cewarta, "cikin yarana 15, guda 2 ne kadai na haifa a asibiti."

Matar, mai shekaru 54 ta ce ba za ta shawarci wata mace ta yi kwatankwacin abinda tayi ba, inda tace "Da ban samu wayewa ba, da yanzu ban tsinci kaina a halin da na ke ba a yanzu."

A cewarta, lokacin da ta haifi yaronta na fari, tana da shekaru 14 a duniya, shekaru fiye da 28 da suka wuce kenan, The Cable ta wallafa.

Hussaina, wacce aka fi sani da 'Maman 15' ta shawarci matan aure da su dinga tsara iyali, saboda tsara yawan yaransu.

KU KARANTA: Ku cigaba da tsananta addu'a a kan masu daukar nauyin Boko Haram, Zulum

A gida na haifa 'ya'ya 13 ba tare da zuwa asibiti ba, mahaifiyar yara 15
A gida na haifa 'ya'ya 13 ba tare da zuwa asibiti ba, mahaifiyar yara 15. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakarun soji sun cafke wani da ake zargi da hada kai da 'yan bindiga

"Cikin yarana mata, wasu sun yi aure, amma babu wacce ta samu ta yi karatu kafin su yi auren. Suna shan bakar wahala, irin rayuwata suke yi," a cewarta.

Ta kara da cewa, "Babu wata uwa da take so ta ga yaranta a cikin wahala, amma bani da yadda zan yi. Yadda nake ganin suna wahala, bana jindadi."

Tace bata taba da na sanin haihuwar yara 15 ba a rayuwarta, duk da 2 cikinsu sun rasu.

A wani labari na daban, bidiyon wata mata yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wanda take bayyana yadda take rabuwa da kawayenta idan ta gano basu da saurayi ko miji.

Kuma ta shawarci duk wasu masu soyayya ko aure, da su rabu da kawayensu marasa masoya.

Lerato N ta ce, "Kawaye marasa samari ko miji mugaye ne, musamman idan suka gano kana tsaka da soyayya".

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng