Ina dakile kawance matukar kawa ta wuce wata 6 babu mashinshini - Matar aure

Ina dakile kawance matukar kawa ta wuce wata 6 babu mashinshini - Matar aure

- Bidiyon wata mata yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wanda take ba wa masu soyayya shawara

- Kamar yadda Lerato tace, ita dai tana rabuwa ne da kawayenta marasa aure ko saurayi gaba daya

- Ta ce hassada tana shiga tsakanin kawaye matsawar suka lura kana soyayya mai burgewa, har su nemi yi maka kwace

Bidiyon wata mata yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wanda take bayyana yadda take rabuwa da kawayenta idan ta gano basu da saurayi ko miji. Kuma ta shawarci duk wasu masu soyayya ko aure, da su rabu da kawayensu marasa masoya.

Lerato N ta ce, "Kawaye marasa samari ko miji mugaye ne, musamman idan suka gano kana tsaka da soyayya".

Ta kara da cewa ta fi so tayi kawance da kawaye wadanda ajinsu ya zama daya da ita, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

KU KARANTA: Da duminsa: Boko Haram sun kaddamar da sabon hari a Gwoza da ke Borno

A cewarta, duk wadanda basu da masoya suna da mugayen halaye kuma ta shawarci duk wata mai saurayi ko miji da kada ta kuskura ta dauki shawarar kawarta wacce bata soyayya.

Ta kara da cewa: "Hassada ce kawai take dawainiya da su. Suna jin takaicin yadda kake da wata baiwa wacce ba su da ita. Don haka ka kiyayi irinsu."

A cewarta, "Kada ka kuskura ka gayyaci kawaye ko abokanka marasa masoya wani taron. Saboda tsaf za su iya jan hankalin naka masoyin, hatta nishadi ba za ka iya yi a gabansu ba."

Ina dakile kawance matukar kawa ta wuce wata 6 babu mashinshini - Matar aure
Ina dakile kawance matukar kawa ta wuce wata 6 babu mashinshini - Matar aure. Hoto daga @uLelato
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku bani lambarsa, ya gamsar da ni matuka - Budurwa da aka yi wa fyade ta roki kotu

A wani labari na daban, Reno Omokri ya yi amfani da shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ya caccaki musulmai a kan zagin Rahama Sadau saboda rigarta mai bayyana tsirarici, amma suka yi shiru a kan satar da 'yan siyasa suke yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel