'Yan Najeriya basu fahimci Mamman Daura ba, Buhari

'Yan Najeriya basu fahimci Mamman Daura ba, Buhari

- Mamman Daura na daya daga cikin mutanen kirkin da mutane ke yi wa mummunar fassara, cewar shugaba Buhari

- Ya ce Mamman yana da halaye nagartattu, kamar hakuri, juriya, fasaha, taimako, jajircewa da kuma dumbin ilimi

- Shugaban kasar ya fadi hakan ne a ranar da Mamman ya cika shekaru 81 a duniya, inda yayi masa fatan alkhairi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Malam Mamman Daura murna a ranar da ya cika shekaru 81 da haihuwa, har yake cewa "Mutane da dama suna yi wa babban dan jaridar mummunar fassara."

Malam Daura dan 'yar uwar Buhari ne kuma babban dan kungiyar Kaduna Mafia ne, taron manyan 'yan kasuwa, ma'aikatan gwamnati, masu fasaha da kuma manyan sojojin arewacin Najeriya.

Shugaba Buhari, ya saki wata takarda ranar Talata ta hannun kakakinsa, Garba Shehu, inda yace "Mutanen Daura yana fuskantar kalubale, saboda duk wani babban mutum ba a yaba wa kokarinsa, hasali ma caccakar jama'a tana bin jijiyoyinsa."

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, shugaban kasar ya ce, "Ba zai yiwu mutum ya zauna tare da Mamman ba, bai karu da ilimi, fasaha da gogewarsa ba."

Shugaban kasar ya ce "cikin halayen Mamman da mutane ba su yaba wa sune saukin kansa, hakuri da jajircewarsa wurin taimakon na kusa da na nesa da shi.

"A yau da kake cika shekaru 81 a duniya, ina fatan Allah ya azurta ka da lafiya da tsawon kwana yayin taimakon Najeriya da al'umma. Kai ne tushen ilimi da fatan al'umma. Muna matukar alfahari da kai."

KU KARANTA: Dakarun soji sun cafke wani da ake zargi da hada kai da 'yan bindiga

'Yan Najeriya basu fahimci Mamman Daura ba, Buhari
'Yan Najeriya basu fahimci Mamman Daura ba, Buhari. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Boko Haram sun kaddamar da sabon hari a Gwoza da ke Borno

A wani labari na daban, dakarun rundunar Operation Lafiya Dole, sun tarwatsa wurin adana man fetur na mayakan ta'addanci na ISWAP a Borno. Kamar yadda hedkwatar tsaro ta wallafa bidiyon, an ga jirgin saman sojin suna tarwatsa ma'adanar man a Tumbun Allura da ke Borno.

A cikin wannan kokarin na dakarun sojin saman ne suka samu halaka wasu mayakan ta'addancin masu yawa. Kamar yadda aka sani, mayakan ta'addanci na ISWAP da Boko Haram sun dade suna cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng