Kotu ta bukaci a tsare dalibin da yayi wa mahaifiyarsa mugun duka

Kotu ta bukaci a tsare dalibin da yayi wa mahaifiyarsa mugun duka

- Wani saurayi mai suna Louis Ekwelor, mai shekaru 23, ya yi wa mahaifiyarsa dukan tsiya

- Ta samu nasarar tserewa da kyar, sannan ta kai kararsa ofishin 'yan sanda da kanta

- Kotu ta yanke masa zama a gidan gyaran hali matsawar bai cika wasu sharudda 2 ba

A ranar Talata, wata kotu da ke Abuja, ta umarci a adana Louis Ekwelor, mai shekaru 23, a gidan gyaran hali, sakamakon dukan mahaifiyarsa da yayi.

Alkali mai shari'a, Hassan Aliyu, ya bayar da wannan umarnin ne matsawar bai cika wasu sharudda 2 ba, Vanguard ta ruwaito.

An bukaci ya kawo wani tsayayye, wanda dole ya zama ma'aikacin gwamnati, wanda yake zaune kusa da kotun, sannan ya bayar da belin rabin miliyan.

Kamar yadda rahotonni suka gabata, babu wani tsayayye da ya gabatar har yanzu.

Alkalin kotun ya dage sauraron shari'ar har sai ranar 16 ga watan Nuwamba.

An kama Ekwealor, mazaunin wuraren Sabongari dake Bwari tare da mahaifiyarsa, da laifi cutar da ita, lamarin da ya musanta.

Lauyan masu gurfanarwa, Idowu Ojo, ta ce mahaifiyar wanda ake zargin, Victoria Ekwealor, da kanta ta kawo karar ofishin 'yan sanda a ranar 14 ga watan Yuli.

Kamar yadda Ojo tace, mahaifiyar ta kawo karar a ranar, inda tace yayi mata dukan tsiya, ya rike adda yana kiranta da mayya. A cewarta, ya yi yunkurin kasheta.

Ta kara da cewa, wurin ceton kanta da kanta, ta bige hancinsa da kasan addar, hakan yasa ya fara habo har ta samu aka zo aka cece ta. Lauyan tace an samu addar lokacin da 'yan sanda suke bincike.

KU KARANTA: Da duminsa: Kamfanin Pfizer ya samar da riga-kafin cutar korona

Kotu ta bukaci a tsare dalibin da yayi wa mahaifiyarsa mugun duka
Kotu ta bukaci a tsare dalibin da yayi wa mahaifiyarsa mugun duka. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Sojin sama sun tarwatsa ma'adanar man fetur ta 'yan ta'adda a Borno

A wani labari na daban, masu garkuwa da mutane sun sace 'dan 'Yar'uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda bayanai suka kammala, masu garkuwa da mutane sun sace Abdullahi, wanda aka fi sani da Yaya Baba, a hanyarsa ta zuwa Kano a titin Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.

Duk da dai ba a samu wani bayani daga 'yan sandan ba, wata majiya mai karfi ta ce basu so maganar ta fito waje ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng