Sabbin mutane 152 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 64,336
- Daruruwan yan Najeriya na sake kamuwa da cutar Korona kulli yaumin
- Gwamnatin tarayya na tsoron adadin masu kamuwa da cutar zai yi tashin gwauron zabi
- Hukumar NCDC ta tsara shirin yadda masu bautan kasa NYSC zasu shiga sansani a fadin tarayya
Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 152 ranar Juma'a a cewar hukumomin kiwon lafiya.
Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 64,336 a Najeriya.
Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Talata , 11 ga watan Nuwamba, 2020.
Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.
Daga cikin mutane sama da 64,000 da suka kamu, an sallami 60,333 yayinda 1160 suka rigamu gidan gaskiya.
KU KARANTA: Wani dan majalisa ya fice daga majalisa yayin da minista ke kare kasafin kudi
Jerin jihohi da Sabbin mutanen da suka kamu –
Lagos-93
FCT-21
Oyo-15
Rivers-11
Bauchi-7
Kwara-2
Bayelsa-1
Edo-1
Plateau-1
KU KARANTA: Ba za a samu rashin abinci a karkashin mulkina ba, Buhari
A bangare guda, Masallacin Harami a ranar Laraba ya karbi kashin farko na masu aikin Umarah daga wajen Saudiyya a mataki na uku na yunkurin dawo da ayyukan Umarah da ziyarar masallatan Harami.
A mataki na uku, masu aikin Umarah 20,000 da masallata 60,000 ake bari shiga masallacin a kowace rana a yunkurin kariya daga annobar Corona don tabbatar da lafiya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng