Da duminsa: Boko Haram sun kaddamar da sabon hari a Gwoza da ke Borno
- A ranar Lahadi, 'yan Boko Haram sun kai hari karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno
- Sojojin sama da na kasa sun mayar da harin 'yan ta'addan cikin gaggawa
- Har yanzu ba a riga an tabbatar da irin barnar da 'yan Boko Haram suka tafka ba
A ranar Lahadi 'yan Boko Haram sun kai hari garin Gwoza da ke jihar Borno, arewa maso gabas ta Najeriya, da tsakar dare, wanda hakan yasa sai da rundunar sojin kasa da ta sama suka yi gaggawar mayar da harin.
Karamar hukumar Gwoza tana kudu maso gabas ta Maiduguri, babban birnin jihar Borno, kuma wuri ne da 'yan ta'adda ke yawan kai wa hari.
Har yanzu ba a tabbatar da irin barnar da ta faru ba sakamakon harin, jaridar HumAngle ta wallafa.
Ta yadda 'yan Boko Haram din da Shekau ya ke jagoranta suke yawan kai hari suka taso wurin, yana nuna matsalar da mazauna wurin suke yawan fuskanta.
Boko Haram sun dade suna kai wa mazauna wurin hari, inda suke kashe mutane ciki har da jami'an tsaro.
Tsakanin 2014 da 2015, sai da Gwoza ta zama matattarar 'yan Boko Haram, amma sojoji sun yi iyakar kokarinsu wurin fatattakar 'yan Boko Haram a watan Maris din 2015, inda mazauna wurin da suka tsere, suka yi ta komawa gidajensu.
Kamar yadda wata kungiyar Likitoci suka bayyana, da babu wani rikici a Gwoza, mutane a kalla 60,000 za su iya zama a garin.
Rayuwa ta yi kunci a garin, ga shi ba a wani samun taimako, saboda sau da yawa sojoji suna kacibus da 'yan Boko Haram.
KU KARANTA: Buhari: Ba zai yuwu mu cigaba da tsame matasa ba wurin yanke hukunci
KU KARANTA: Da gangan na dinga lalata da kanwar matata don in bata mata rai - Magidanci
A wani labari na daban, Jaridar Leadership ta wallafa cewa, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan Najeriya wadanda har ya zuwa yanzun basu lashi romon gwamnatinsa ba, da kuma wadanda su ke ganin gazawar gwamnatin, da su yi hakuri.
Ya yi wannan roko a ranar Juma'a a garin Ilorin a wurin taron fadi-ra'ayinka. Taron wanda an yi shi ne saboda zanga-zangar EndSARS da kuma sakamakon da ta haifar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng