Da duminsa: Allah ya yiwa Dan Iyan Zazzau, Alhaji Yusuf Ladan, rasuwa

Da duminsa: Allah ya yiwa Dan Iyan Zazzau, Alhaji Yusuf Ladan, rasuwa

- Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!

- Kwana daya bayan nadin sabon sarki, Dan iyan Zazzau ya rasu

- Ya rasu bayan rashin lafiyan da yayi fama da shi

Allah ya yiwa Dan Iyan Zazzau, Alhaji Yusuf Ladan, cikawa da safiyar Talata, 10 ga watan nuwamba, 2020.

Alhaji Yusuf Ladan ya rasu a gidansa da ke Kaduna bayan gajeruwar fama da rashin lafiya.

Dan Iyan Zazzau ya rasu bayan shekaru 86 a duniya.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa za a yi sallar jana’izarsa bayan sallar Azahar a Masallacin Juma’a na Maiduguri Road, jihar Kaduna.

A lokacin rayuwarsa, Marigayi Alhaji Yusuf Ladan ya kasance fitaccen dan jarida, tsohon Manajan Hukumar Gidajen Rediyo da Talabijin na Jihar Kaduna (KSMC).

KU KARANTA: Ba zamu iya cire rubutun larabcin dake cikin takardar Naira ba - CBN

Da duminsa: Allah ya yiwa Dan Iyan Zazzau, rasuwa
Da duminsa: Allah ya yiwa Dan Iyan Zazzau, rasuwa Credit: Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA:Yadda ake bikin mika sandar sarautar Zazzau ga sabon Sarki

A wani labarin, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana halaye 9 wadanda suka dace da na sarakunan addini da suka janyo ya nada Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, a matsayin sarkin Zazzau.

Yayin da gwamnan yayi jawabi wurin kaddamar da nadin sabon sarkin da kuma gabatarwa da sarkin ma'aikatan fadarsa da aka yi a ranar Litinin a Zaria, gwamnan ya ce halayen sabon sarkin masu ban sha'awa sun hada da fasaha, ilimi, tausayi, kirki, kyakkyawar mu'amala, sanin yakamata, hakuri da juriya.

Kamar yadda gwamnan yace, ba wadannan kadai ne halayen Bamalli na kirki ba, har da dagewa wurin yin aiki tukuru a duk wuraren da ya taba yin aiki, don haka ya zama abin alfaharin masarautar da jihar gabadaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel