Korona ta kama gwamnan APC a arewa bayan fargabar sake dawowar cutar a karo na biyu

Korona ta kama gwamnan APC a arewa bayan fargabar sake dawowar cutar a karo na biyu

- Ana fargaba tare da tsoron cewa annobar korona za ta sake dawowa a karo na biyu

- Wasu kasashen Turai da suka hada da kasar Ingila sun sanar da sake saka dokar kulle domin dakile yaduwar cutar

- A farkon zuwan annobar, dukkan kasashen duniya sun dauki matakai domin dakile yaduwarta a tsakanin jama'a

Gwamnan jihar Niger Abubakar Sani Bello ya kamu da cutar sarƙewar numfashi wadda aka fi sani da Korona.

Hukumar kare yaɗuwar cututtuka (NCDC) ta sanar da sake kamuwar mutane 300 da suka kamu da kwayar da cutar Korona a Najeriya, ranar Lahadi.

Wannan ya haifar da firgicin cewa annobar ta na kokarin sake dawowa a karo na biyu.

Gwamnan jihar Niger ya kamu da kwayar cutar Korona, ya sanar da hakan ne da kansa a wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na Tiwita.

"Sakamakon Gwajin da akayi min ya nuna na kamu da cutar Korona, duk da ba wata alama da ta bayyana a fili, amma tuni na killace kaina" a cewarsa.

Korona ta kama gwamnan APC a arewa bayan fargabar sake dawowar cutar a karo na biyu
Abubakar Sani Bello
Asali: Twitter

In zaku iya tunawa, hukumar kare yaɗuwar cututtuka (NCDC) ta yi gargaɗin sake ɓullar cutar a karo na biyu, inda ta sanar da ,adadin da ya kai mutum 300 a matsayin sabbin waɗanda suka kamu da cutar a yinin Lahadi

Tu ni mutane suka fara shiga firgici da razanin sake ɓullar cutar a karo na biyu, wanda hakan ke nufin cewa za a kara daukan matakan dakile yaduwarta a tsakanin jama'a, kamar yadda aka yi a karo na farko.

Bayan bullar cutar korona a farkon shekarar 2020, kasashe sun dauki matakan dakile yaduwar korona ta hanyar saka doka kulle tare da bawa jama'a shawarar su nesanta da juna tare da yawaita wanke hannaye.

Dokar kulle ta saka kunci a zukatan jama'a saboda hana kasuwanni, kasuwanni, masana'antu da zirga-zirgar jama'a a manyan tituna da cikin lunguna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng