Sakataren tsaro na Trump Mark Esper ya shirya takardar murabus dinsa kafin a kammala zabe

Sakataren tsaro na Trump Mark Esper ya shirya takardar murabus dinsa kafin a kammala zabe

- Wata majiya ta tabbatar da cewa shirin murabus din sakataren tsaro na Shugaba Donald Trump, Mista Mark Esper ya yi nisa

- Mai magana da yawun Mista Esper din ya ce ba murabus zai yi ba kuma ba wanda ya umarce shi da yin murabus

- Amurkawa na ci gaba da sauraren sakamakon zaben da zai fayyace musu shugaban kasar na 46

Sakataren tsaron Trump, Mark Esper ya tsara rubuta takardar murabus yayin da yan Kasar Amurka ke jiran sakamakon zaben shugaban kasa a cewar rahoton LIB.

Gidan jaridar NBC sun ruwaito cewa Esper ya shirya haka ne "saboda yana cikin wanda aka dade ana zargin za a sallama bayan zabe."

Sakataren tsaro na Trump Mark Esper ya shirya takardar murabus dinsa kafin a kammala zabe
Sakataren tsaro na Trump Mark Esper ya shirya takardar murabus dinsa kafin a kammala zabe. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa

Dangantaka ta dade da yin tsami tsakanin Shugaba Donald Trump da Esper bisa dalilai da dama ciki har da amfani da jami'an tsaro wajan kwantar da zanga zanga a baya bayan nan.

Rahotan ya bayyana cewa a halin yanzu Esper ne ke taimakawa wajen cire sunayen shugabanni Soji da suka yi yaki don ganin ba a haramta bautar da bakaken fata ba a kasar.

A rahoton kwararru, a satin nan, Esper ya mika bukatar sa a rubuce ga shugabanni a Pentagon akan a sake Sunayen Jiragen ruwa dana titunan dake dauke da sunayen manyan sojoji.

Lamarin da ka iya ta'azzara dangantaka tsakanin sa da Trump, a cewar rahoton.

DUBA WANNAN: Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona

NBC ta tabbatar da rahoton daga majijoyi da dama, amma mai magana da yawun Mr. Esper ya fadawa duniya cewa ba murabus zai yi ba.

Mai magana da yawun Pentagon Jonathan Hoffman ya kira rahoton NBC da cewa "ba dai dai bane kuma ya saba ta hanyoyi da dama," yana mai cewa Esper bashi da wani yunkuri na murabus kuma ba'a bashi umarnin mika takardar ajiye aiki ba.

"Shine dai har yanzu Sakataren tsaron Shugaban kasar kuma yana aiki tukuru wajen inganta harkokin tsaro", Hoffman ya wallafa a Tuwita.

Har yanzu dai, Amurkawa na dakon sakamakon zaben shugaban kasa da zai fayyace wanda zai zama shugaban kasar na 46.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel