Gobe za'a rantsar da sabbin Alkalan kotun koli takwas

Gobe za'a rantsar da sabbin Alkalan kotun koli takwas

- Majalisar dattawa ta amince da sunayen mutane takwas da shugaba Buhari ya gabatar domin nadasu matsayin Alkalan Kotun Koli

- Wadannan Alkalan sun kasance masu aiki a kotun daukaka kara kafin yanzu

- Daga ciki akwai wanda ya zauna kan shari'ar zaben Buhari da Atiku

Sabbin Alkalan kotun kolin takwas da shugaba Buhari ya zaba zasu yi ranstuwar fara aiki ranar Juma'a, 05 ga watan Nuwamba, 2020.

Shugaban Alkalan Najeriya, CJN Tanko Muhammad, ne zai rantsar da su, The Nation ta ruwaito.

An samu labarin cewa an shirya taron ratsuwar karfe 10 na safe, a farfajiyar kotun koli.

Sabbin Alkalan da aka karawa girma daga kotun daukaka kara zuwa kotun koli sune Helen Ogunwumiju (Kudu masu yama); Emmanuel Agim (Kudu maso Kudu); Lawal Garba, (Arewa maso yamma); Abdu Aboki (Arewa maso yamma), da M M Saulawa (Arewa maso yamma).

Sauran sune Adamu Jauro (Arewa maso gabas); Samuel Oseji (Kudu maso kudu) da Tijani Abubakar (Arewa maso gabas).

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada su ne bayan da majalisar shari'a ta zabesu kuma majalisar dattawa ta tabbatar da su ranar 13 ga Oktoba.

KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 214, Biden 264

Gobe za'a rantsar da sabbin Alkalan kotun koli takwas
Gobe za'a rantsar da sabbin Alkalan kotun koli takwas
Asali: UGC

A wani labarin daban, wani mutumi mai suna Dahiru Buba, wanda yayi tattaki domin murnar nasarar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yayi a zaben 2015 ya na fama da ciwon kafa.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Buba na neman taimakon jama'a saboda kafar ta tasa shi gaba.

Dahiru Buba, wanda dan asalin Karamar Hukumar Dukku ne a Jihar Gombe, yana daya daga cikin mutanen da suka yiwa shugaba Buhari tattaki daga jihohinsu zuwa birnin tarayya Abuja.

SHIN KO KA DUBA NAN: Daga satar babur, kotu ta yanke hukuncin rataya ga wani mutum

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel