2023: Jihohin tsakiya ba za su bi ra'ayin arewa ba - Bitrus ya tabbatar

2023: Jihohin tsakiya ba za su bi ra'ayin arewa ba - Bitrus ya tabbatar

- Kungiyar jihohin tsakiyan Najeriya (MBF) ta ce ba za ta amince da dan arewa a matsayin dan takarar shugaban kasa ba

- Shugaban kungiyar, Pogu Bitrus, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da manema labarai suka yi da shi a Kaduna

- A ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba ya ce lallai sai dai su gabatar da dan takarar shugaban kasa daga bangarensu

Kungiyar jihohin tsakiyar Najeriya (MBF) sun ce ba za su amince da dan arewa a matsayin shugaban kasar Najeriya ba a 2023.

Pogu Bitrus, shugaban MBF yace lallai su za su tsayar da dan takarar shugaban kasa a 2023.

Bitrus ya ce sun ja layin zaben wani dan arewa a wani matsayi na siyasa.

Bangarori daban-daban suna ta shirye-shiryen zaben shugaban kasa da ke gabatowa don tsayar da wani daga wurinsu a matsayin dan takarar shugaban kasar Najeriya.

Shugaban kungiyar jihohin tsakiyan Najeriya (MBF), Pogu Bitrus, ya ce ba za su yarda a tsayar da wani dan arewa ba a matsayin dan takarar shugaban kasa ba.

Jaridar The Sun ta ce Bitrus ya ce MBF sun yanke hukuncin zabar dan takarar shugaban kasa daga bangarensu saboda suna bukatar tsarin karba-karba.

Ya sanar da hakan ne a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai bayan kammala wani taro a Kaduna.

KU KARANTA: Sabon bidiyon Shekau: Karamin yaro rike da bindiga yana barazanar tabbatar da tashin hankali

2023: Jihohin tsakiya ba za su bi ra'ayin arewa ba - Bitrus ya tabbatar
2023: Jihohin tsakiya ba za su bi ra'ayin arewa ba - Bitrus ya tabbatar. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ciyar da 'yan makaranta: Ganduje yana kashe N4bn kowacce shekara - Kwamishina

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kano wacce Gwamna Abdullahi Ganduje yake jagoranta ta ce tana kashe naira biliyan 4 duk shekara wurin ciyar da daliban makarantar kwana da ke jihar.

Kwamishinan ilimi, Sunusi Kiru, ya sanar da hakan ga manema labarai a kan nasarorin da ma'aikatar ta samu cikin watanni 12, Channel TV ta wallafa.

Ya ce gwamnatin Ganduje ta fi bayar da muhimmanci ga ilimi, musamman yadda yasa shi ya zama kyauta kuma tilas a kan kowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel