Ciyar da 'yan makaranta: Ganduje yana kashe N4bn kowacce shekara - Kwamishina
- Gwamnatin jihar Kano wacce Ganduje ke jagoranta ta ce tana kashe naira biliyan 4 duk shekara wurin ciyar da 'yan makarantun kwana
- Kwamishinan ilimi, Sunusi Kiru ya sanar da hakan ranar Talata a wata hira da yayi da manema labarai a kan nasarorin gwamnatin
- Ya ce yanzu haka ana nan ana karasa ginin makarantu 5 a masarautu 5 da ke jihar, Masarautar Kano, Gaya, Karaye, Rano da Bichi
Gwamnatin jihar Kano wacce Gwamna Abdullahi Ganduje yake jagoranta ta ce tana kashe naira biliyan 4 duk shekara wurin ciyar da daliban makarantar kwana da ke jihar.
Kwamishinan ilimi, Sunusi Kiru, ya sanar da hakan ga manema labarai a kan nasarorin da ma'aikatar ta samu cikin watanni 12, Channel TV ta wallafa.
Ya ce gwamnatin Ganduje ta fi bayar da muhimmanci ga ilimi, musamman yadda yasa shi ya zama kyauta kuma tilas a kan kowa.
Kwamishinan ya bayyana ginin makarantu 5 a masarautar Kano, Gaya, Karaye, Rano da Bichi sun kusa kammaluwa.
Ana sa ran komawa makarantu daga watan Janairun 2021, tare da sababbin dalibai 360 a kowacce makaranta.
"Gwamnatin jihar ta samar da wata babbar makarantar sakandare ta fasaha da ke garin Ganduje, a karamar hukumar Dawakin Tofa.
"Yanzu haka ana cigaba da karasa ginin katangu, azuzuwa 6, mota mai daukar mutane 32 da wata motar kirar Hilux don zirga-zirgar makarantar," cewar Kiru.
KU KARANTA: Nsukka: Gwamnan Enugu ya bada umarnin gaggauta sake gina masallatai
KU KARANTA: Tsaro da satar kayan tallafi: Gwamnonin Najeriya za su yi muhimmin taro
A wani labari na daban, babban faston nan da ke jihar Enugu, Mbaka, ya ce zanga-zangar EndSARS ba don zaluncin 'yan sanda aka yi ta ba, an yi ta ne saboda mulkin kama-karya, The Cable ta wallafa.
Ya fadi hakan ne a majami'a a ranar Lahadi, inda yace ya kamata shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya gafarar zaluncin da shugabannin da suka gabata suka yi da kuma nasa kura-kuren.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng