Dalilin da yasa gidajen gyaran hali basu karbar sabbin masu laifi - Ministan cikin gida

Dalilin da yasa gidajen gyaran hali basu karbar sabbin masu laifi - Ministan cikin gida

- Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce ma'aikatan gidan gyaran hali sun ki amsar wadanda 'yan sanda suka maido suna zargin fursinonin da suka tsere ne

- Ya ce ma'aikatan sun bayar da dalilin daukar wannan matakin, suka ce soboda 'yan sandan ba su bi ka'idoji da dokokin kare kai daga cutar COVID-19 ba

- Ministan ya sanar da hakan ne bayan ya gabatar da kasafin ma'aikatarsa na 2021, inda ya bukaci karin kudi domin gyaran gidajen gyaran halin

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce ma'aikatan gidan gyaran hali suna ta korar wadanda 'yan sanda ke kawo musu a matsayin wadanda ake zargin fursinoni ne suka gudu, saboda rashin kiyaye dokar COVID-19 kamar yadda gidajen gyaran halin suka bukata.

Ministan ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya gama gabatar da kasafin ma'aikatarsa ta 2021 a gaban kwamitin majalisar dattawa.

A cewarsa: "Yan sandan basu kula da hanyoyin kare kai daga kamuwa daga cutar COVID-19 yayin mayar da wadanda ake zargin fursinoni ne suka tsere.

"Ya ce ma'aikatarsa ta bukaci karin kudi don gyaran gidajen gyaran halin da masu zanga-zangar EndSARS suka lalata."

KU KARANTA: Mbaka ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya hakuri a kan mulkin kama karya

Dalilin da yasa gidajen gyaran hali basu karbar sabbin masu laifi - Ministan cikin gida
Dalilin da yasa gidajen gyaran hali basu karbar sabbin masu laifi - Ministan cikin gida. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 75, sun rasa sojoji 3 a Borno

A wani labari na daban, Gwamnoni 36 na Najeriya za su yi taro ranar 4 ga watan Nuwamba 2020 a kan yadda za su shawo kan matsalolin da ke addabar Najeriya, Daily Trust ta wallafa hakan.

Gwamnonin za su yi amfani da damar don tattaunawa a kan yadda za a yi da rundunar SARS da aka rushe, wadanda ayyukansu suka yi sanadiyyar zanga-zanga a cikin jihohin Najeriya.

Sannan za su tattauna a kan yadda aka wawushe kayan tallafin COVID-19 a ma'ajiyoyin gwamnati da ke jihohi daban-daban. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel