Gwamnonin Arewa sun sha alwashin tabbatar da hadin kan Najeriya
- A ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba gwamnonin arewa suka yi wani taro a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna
- Ba gwamnoni kadai suka je taron ba, ministoci, manyan sarakuna, jami'an tsaro da sauran manyan mutane a arewa sun samu halarta
- Sun tattauna a kan duk wasu matsalolin arewa kamar zanga-zanga, ASUU, kafafen sada zumunta da yadda za'a shawo kansu
A ranar Litinin gwamnonin arewa suka yi kushe a kan zanga-zangar EndSARS, da kuma sauran al'amura da za su tayar da tarzoma, inda suka ce duk wanda ke neman canji bayan zabe to yayi zanga-zangar lumana.
Gwamnonin sun roki mutane da su hada kai da nuna kaunar juna tsakanin 'yan Najeriya, Vanguard ta ruwaito.
Sun fadi hakan ne a wata takarda da shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya karanta bayan wani taro da suka yi a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna.
Sakataren gwamnatin tarayya, shugaban ma'aikatan shugaban kasa, ministoci, sarakunan arewa da sauran manyan mutane sun samu damar halartar taron.
KU KARANTA: Iyaye da 'yan uwa sun mayar da 'yan gidan fursuna 24 zuwa gidan kaso a Benin
Takardar da aka rubuta a ranar 2 ga watan Nuwamba ta kunshi abubuwa da dama wadanda za a yi don kawo cigaba a arewa. Inda suka mika jinjinarsu ga shugabannin gargajiya a kan babbar rawar da suka taka wurin dakatar da matasan arewa daga yin zanga-zangar EndSARS.
Sun tattauna yadda za su kawo hadin kai da cigaba a kasa. Sannan sun tattauna a kan yadda mutane ke yada labaran bogi a kafafen sada zumuntar zamani.
Sun tattauna a kan yadda za a sanya ido a babban birnin tarayya don gudun cigaba da lalata dukiyoyin gwamnati.
Sannan sun shawarci majalisar dattawa da su dinga hanzarin dakatar da duk wata zanga-zanga a cikin kasa. Kuma sun tattauna bukatar yin gaggawar daidaitawa da ASUU don dalibai su koma makarantunsu.
KU KARANTA: Namijin kishi: Fasto da mataimakiyarsa sun kone bayan saurayi ya ban ka wa gidan budurwa wuta
A wani labari na daban, Augustine Yiga, shararren faston nan na Uganda ya mutu, Jaridar The nation ta wallafa.
Faston ya rasu ne bayan watanni 5 da kama shi da laifin yayata cewa Coronavirus zazzabi ne wanda dama aka dade ana yinsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng