Sojan Najeriya ya zane budurwa a kan shigar banza, ya aske ladabtar da matashi saboda askin kansa

Sojan Najeriya ya zane budurwa a kan shigar banza, ya aske ladabtar da matashi saboda askin kansa

- Sojoji suna aske gashin kan maza masu tara gashi da kuma zane mata masu damammun tufafi a Ibadan

- A yau ne aka wayi gari ana ganin bidiyoyin hakan yana ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani

- Sojojin sun tsaya ne daidai wurin Beere da ke cikin babban birnin jihar Oyo suna wannan aikin a bisa umarnin gwamnan

Sojoji suna zane mata masu shigar banza da kuma maza masu tara gashin kai a wuraren Beere da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Idan baku manta ba, sakamakon guguwar zanga-zangar EndSARS a jihar, Gwamna Seyi Makinde, ya nemi sojoji su tsaya wuri-wuri a jihar don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A bidiyon da yayi ta yawo, an ga sojoji da bulalai suna zane mata masu matsatsun riguna da ke bayyanar da surorin su a titin Beere.

An ga wani bidiyo da ke nuna sojojin suna aske gashin maza masu tara gashi.

Daya daga cikin wadanda al'amarin ya faru dashi ya wallafa yadda sojoji suka ci zarafinsa kuma suka aske masa gashi.

KU KARANTA: Dakarun soji sun kashe 'yan ta'adda, sun bankado harin tawagar 'yan gudun hijira

Matashin mai suna PrimalHubLtd yace: "Barkanmu 'yan Najeriya, na lura sojoji sun rude. Nazo in bayyana muku artabun da muka yi da su a hanyata ta dawowa daga coci wuraren Bodija da ke Ibadan, wanda sai da na biyo ta wurin Beere inda na samu sojojin suna wurin da Gwamna Seyi makinde ya umarcesu da su tsaya.

Sojan Najeriya ya zane budurwa a kan shigar banza, ya aske ladabtar da matashi saboda askin kansa
Sojan Najeriya ya zane budurwa a kan shigar banza, ya aske ladabtar da matashi saboda askin kansa. Hoto daga @dailynigerian
Asali: Twitter

"Sai da suka daukeni da mari tukunna nayi biyayya ga umarninsu don gudun cin mutunci. Ina mamaki idan tsawon gashi na nuna mutum dan ta'adda ne ko kuma mai laifi ko barawo. Hakika mutanen nan basu da fahimta, amma yakamata a ce an duba kwakwalwar kowanne soja."

KU KARANTA: Da duminsa: EFCC ta yi wa tsohon shugaban FIRS kiran gaggawa

A wani labari na daban, a wata takarda ta ranar Juma'a, Bisi Kazeem, Kakakin hukumar FRSC yace shugaban hukumar, Boboye Oyeyemi, ya bayar da umarni, inda yace jami'an FRSC su cigaba ta kula da tituna yadda ya dace.

Ya bayar da wannan umarnin ne bayan mutane 21 sun rasa rayukansu bayan wata babbar mota ta murkushe wata motar 'yan makaranta a jihar Enugu, The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel