Namijin kishi: Fasto da mataimakiyarsa sun kone bayan saurayi ya ban ka wa gidan budurwa wuta
- Wani mutum mai shekaru 40, mai suna Obukulubu ya banka wa gidan budurwarsa wuta saboda tsananin kishi
- Sai dai ta tsallake rijiya da baya, inda wani fasto da wata yarinya da ke gidan suka kone har lahira
- Ya aikata hakan ne saboda yana zargin tana tarayya da wani, don haka ya jira karfe 3 na dare tayi ya kona ta
Wani dan shekara 40 mai suna Etifa Obukulubu, ya banka wa gidan da ke wuraren igbogene, karamar hukumar Yenagoa, wuta a ranar Asabar saboda zargin budurwarsa tana tarayya da wani.
Sakamakon wutar, wani fasto da ke aiki da sabuwar cocin Baptist da wata yarinya sun kone har lahira.
Kamar yadda aka tattaro bayanai, al'amarin ya faru ne da karfe 3:00 na daren ranar Lahadi, wanda jama'a suka yi ta kokarin kashe wutar amma abin yaci tura.
Lokacin da budurwar, mai suna Wilberforce za ta bar gidan don bai wa faston ya kwana, ashe ta kulle dayar kofar gidan ta baya, wanda hakan ya hana marigayin damar fita.
KU KARANTA: Saurayi ya biya wa budurwa 432,000 a mashaya, ta ki sauraronsa kuma ta bi wani saurayi
Mazauna unguwar Igbogene sun sanar da LEADERSHIP cewa, saurayin da ake zargin yin wannan aika-aikar, yayi ta jiran budurwar ta koma gida, kawai sai ya ganta da wani mutum tare da wata yarinya, takaicin haka ya ingiza shi ya kona gidan. Ya jira su shiga gidan ne gabadayansu don ya banka musu wuta da fetur.
Sai dai bai san cewa budurwar tasa ta tafi wurin kawarta don ta kwana ba. Wani mazaunin wurin ya ce al'amarin ya ba kowa mamaki. Saboda gidaje 3 ne suka raba gidajen masoyan, kuma babu wanda yayi tunanin soyayya suke yi.
Sai dai kowa yaji takaicin yadda faston da mataimakiyarsa suka rasa rayukansu sakamakon wutar. An gayyaci faston ne don yin wa'azi a Yenagoa, sai budurwar ta ara masa gidanta don ya kwana, alabarshi sai ya tafi da sassafe, ashe tsautsayi na biye.
KU KARANTA: Salamatu Abubakar: Mahaifiyar yara 3 da ke fentin mota a matsayin sana'a
A wani labari na daban, gwamnati ta kafa kungiyar bincike a kan kisan gillar da ake zargin sojoji sun yi wa masu zanga-zangar SARS da aka rushe, inda suka kai ziyara asibitin sojoji da ke Falomo, wurin Ikoyi a jihar Legas.
Da farko an hana masu binciken shiga harabar asibitin na tsawon mintuna 30. Bayan an barsu sun shiga harabar, an kai su wurin da aka ce asibitin sojoji ne.
Masu binciken sun shiga har bayan asibitin, wuraren wani kango.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng