Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna)

Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna)

- Shahararren faston nan na kasar Uganda mai suna Augustine Yiga ya kwanta dama

- Ya rasu ne watanni kadan bayan an kama shi da laifin yada jita-jita a kan COVID-19

- Faston ya rasu ne sakamakon fama da yayi da ciwon hanta

Augustine Yiga, shararren faston nan na Uganda ya mutu, Jaridar The nation ta wallafa.

Faston ya rasu ne bayan watanni 5 da kama shi da laifin yayata cewa Coronavirus zazzabi ne wanda dama aka dade ana yinsa.

Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna)
Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna). Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

Faston cocin Revival da ke Kawaala, a Kampala, wanda aka fi sani da Abizaayo, ya rasu ne a ranar 26 ga watan Oktoba, a asibitin Nsambya inda aka kwantar dashi sakamakon fama da ciwon hanta.

An kawo gawarsa cocin a ranar Asabar, 31 ga watan Oktoba da rana.

Za'a rufeshi ranar Lahadi kusa da mahaifiyarsa.

Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna)
Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna). Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakarun soji sun kashe 'yan ta'adda, sun bankado harin tawagar 'yan gudun hijira

Kamar yadda ya bayar da wasiyya, ya na so a wuni ana nuna burniyarsa a gidan talabijin na ABS.

Mutuwarsa ta zo bayan watanni 5 da kama shi da yada labaran bogi da jita-jita a kan COVID- 19.

A satin da ya gabata, wasu mutane a kafafen sada zumuntar zamani suka yi ta yada labarin mutuwarsa, amma daga baya iyalinsa suka karyata labarin, inda suka ce yana nan da ransa.

Dansa, Andrew Jjengo yace faston ya dade bashi da lafiya.

Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna)
Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna). Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: FRSC ta umarci jami'anta da su koma kan tituna

A wani labari na daban, wani mutum mai suna London Akan, ya bayyana yadda ya tatike asusun bankinsa wurin biyawa wata budurwa Naira 432,000 da ta kashe a wata mashaya.

yadda yace, ya hango wata kyakkyawar budurwa mai sura, zaune tare da kawayenta a mashayar, The Nation ta wallafa.

Don ya samu gurbi a zuciyarta, sai ya yanke shawarar biyan duk kudaden da budurwar da kawayenta suka kashe, kwatsam aka sanar dashi sun kashe Naira 432,000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel