An kwace zanga-zangar EndSARS ne don raba Najeriya - Shugabannin Arewa
- Ba zamu gushe muna ganin cewa ba'a raba kasar nan ba,Shugabannin Arewacin Najeriya
-- Shugabannin sun hada da gwamnoni, sarakunan gargajiya, shugabannin majalisar dattawa da mataimakin kakakin majalisa
- Za su dauki mataki kan lamarin almajiranci a a Arewacin Najeriya
A murya daya ranar Litinin, Arewa ta yi Alla-wadai na zanga-zangar #EndSARS saboda an shiryata ne domin raba Najeriya.
Yankin Arewa da shugabanninta sun ce wasu sun kwace zanga-zangar kuma sun yi amfani da ita wajen lalata, sace-sacen dukiyan gwamnati da na jama'a.
Hakazalika sun yi yunkurin yiwa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari juyin mulki.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ne ya jagoranci zamar.
Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Simon Lalong, ya yi jawabi kan abubuwan da aka tattauna a zaman da ya gudana a jihar Kaduna.
Yace: "A zaman nan, an yi Alla-wadai da abubuwan da suka faru a zanga-zangar EndSARS. Wasu kiraye-kiraye da manufofi na daban irin na juyin mulki suka kwace zanga-zangar."
"A ganawar an jaddada cewa ba za'a yarda kasar nan ta rabu ba."
KU KARANTA: Shugabannin Amurka 10 kacal suka fadi a zaben tazarce a tarihi, da alamun Trump zai zama na 11 (Ga jerinsu)
KU KARANTA: Kannywood: Babban darakta Falalu dorayi ya yi wa Rahama Sadau shagube a kan shigar da ta yi
Ga jerin wadanda suka halarci taron:
Gwamna Malam Nasir El-Rufa’I (Kaduna), Simon Lalong (Plateau), Aminu Tambuwal (Sokoto), Bello Matawale (Zamfara), Atiku Bagudu (Kebbi), Abdulrahman Abdulrazak (Kwara), Governor Sani-Bello (Niger), Governor Yahaya (Gombe),, Alhaji Nasiru Gawuna,Alhaji Mannir Yakubukatsina)
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari; shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan; mataimakin kakakin majalisa, Ahmed Wase; Sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu; ministan labarai, Lai Mohammed; da ministan birnin tarayya, Mohammed Bello.
Sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad; Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero; Sarkin Zazzau, Alhaji ahmed Bamalli; Etsu Nupe. Alhaji Yahaya Abubakar; Sarkin Ilori, alhaji Ibrahim Gambari; Sarkin Bauchi, Sarkin Fika, Sarkin Hadejia, Sarkin Lafita dss.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng