Abubuwa 4 da ka iya sa Donald Trump shan kaye a zaben Amurkan yau Talata

Abubuwa 4 da ka iya sa Donald Trump shan kaye a zaben Amurkan yau Talata

Bayan kimanin shekaru hudu a ofis a matsayin shugaban kasar Amurka, Donlad Trump, na bukatan yan kasar su sake zabensa karo na biyu a zaben dake gudana yau.

Babban abokin hamayyarsa a zaben da ke gudana yanzu haka shine dan takaran jam'iyyar Democrat, Joe Biden.

Legit.ng ta zakulo muku wasu kura-kurai da ka iya sabbabawa Donald Trump shan kaye a zaben:

1. Siyasantar da annobar Coronavirus

Salon da shugaba Trump ya dauka wajen yaki da cutar Korona na iya zama babban dalilin da ya sa wasu ba zasu zabeshi ba.

Misali, lokacin da shugabannin kasashen duniya ke daukan matakai masu tsauri domin dakile cutar, Trump ya siyasantar da lamarin kuma yayi mata rikon sakainar kashi.

A bisa binciken Pew, shugaba Trump ya yi jinkiri wajen daukan mataki.

Kawo yanzu mutane 230,000 suka rasa rayukansu sakamakon cutar, Worldometer ta ruwaito.

2. Kalaman wariyar launin fata

Shugaba Trump ya shahara wajen kalamai dake ishara zuwa ga wariyar launin fata kuma bakaken fara musamman na iya zaben abokin hamayyarsa, Biden.

Abubuwa 4 da ka iya sa Donald Trump shan kaye a zaben Amurkan yau Talata
Abubuwa 4 da ka iya sa Donald Trump shan kaye a zaben Amurkan yau Talata Credit: @realDonaldTrump
Asali: Twitter

KU KARANTA: An kwace zanga-zangar EndSARS ne don raba Najeriya - Shugabannin Arewa

3. Saba alkawari

Akwai wasu alkawuran zabe masu muhimmanci ta Trump bai cika ba har yanzu kuma hakan na iya zama matsala.

Daga cikin alkawuran shine gina bango tsakanin Amurka da Mexico wanda har yau ya gaza.

Hakazalika ya yi alkawarin soke tsarin Obamacare kuma ya maye gurbinta da sabon tsari. Ya soke ta amma bai maye gurbinta da wani tsarin ba.

4. Yaki da yan gudun hijra

Sabbin ka'idojin yan gudun hijra da Trump ya samar zai isa sa mazauna kasar wadanda ba yan asali bane watsi da shugaban kasan.

Tun lokacin da ya hau mulki, Trump ya haramtawa wasu yan kasashe shiga Amurka gaba daya. Yawancin kasashen Larabawa ne.

Bayan haka ya fara raba iyaye da yaransu saboda iyayen ba yan Amurka bane amma sun haifi yaran a Amurka.

Mun kawo muku cewa a tarihin Amurka, shugabannin kasa suna samun nasarar tazarce bayan karewar wa'adinsu na farko saboda irin ayyukan da suka yi.

Amma ba haka ake gani tattare da Donald Trump ba saboda lokacin da ya kaddamar yakin neman zabensa a 2019, maki 43% kadai ya samu, cewar Gallup.

Business Insider ya bayyana cewa tun daga lokacin makin ke cigaba da sauka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng