Shugabannin Amurka 10 kacal suka fadi a zaben tazarce a tarihi, da alamun Trump zai zama na 11 (Ga jerinsu)
- Shugabannin kasar Amurka 10 kadai suka ta fadi a zabe a tarihin kasar
- Zabubbuka sun nuna cewa da kamar wuya Trump ya lashe zaben bana saboda yadda ya jagoranci yaki da cutar COVID-19
- Trump na bibiyan Biden a kuri'un da aka kada kawo yanzu a manyan jihohi
A tarihin Amurka, shugabannin kasa suna samun nasarar tazarce bayan karewar wa'adinsu na farko saboda irin ayyukan da suka yi.
Amma ba haka ake gani tattare da Donald Trump ba saboda lokacin da ya kaddamar yakin neman zabensa a 2019, maki 43% kadai ya samu, cewar Gallup.
Business Insider ya bayyana cewa tun daga lokacin makin ke cigaba da sauka.
Binciken Gallup a watan Satumba da Oktoba ya nuna cewa makin da Trump ya samu bai wuce 42% zuwa 44%
Watanni baya, bincike ya nuna cewa da wuya Trump ya zarce saboda matsin tattalin arzikin da kasar ta shiga da kuma yadda Trump ya gudanar da yaki da cutar COVID-19.
Trump na bayan Biden a manyan jihohi irinsu Michigan, Wisconsin, Pennsylvania da Florida, duk da cewa ya lashe wadannan jihohi a zaben 2016.
A karshe, Trump na iya shiga jerin shugabannin Amurka da suka fadi a zabe.
KU KARANTA: Kannywood: Babban darakta Falalu dorayi ya yi wa Rahama Sadau shagube a kan shigar da ta yi
KU KARANTA: Taron NGF: Sarki Ahmad Bammali zai jagoranci kwamitin matasa da kungiyoyi
Ga jerin tsaffin shugabannin Amurka da suka fadi a zaben tazarce:
1. John Adams (1797-1801)
2. John Quincy Adams (1825-1829)
3. Martin Van Buren (1837-1841)
4. Grover Cleveland (1885-1889)
5. Benjamin Harrison (1889-1893)
6. William Howard Taft (1909-1913)
7. Herbert Hoover (1929-1933)
8. Gerald Ford (1974-1977)
9. Jimmy Carter (1977-1981)
10. George H.W. Bush (1989-1993)
A yau, Talata, 13 ga Nuwamba, zaben shugaban kasan Amurka ke gudana: Yan Amurka sun fito kwansu da kwarkwatansu domin zaben shugaban da zai jagorancesu shekaru 4 masu zuwa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng