Dakarun soji sun kashe 'yan ta'adda, sun bankado harin tawagar 'yan gudun hijira

Dakarun soji sun kashe 'yan ta'adda, sun bankado harin tawagar 'yan gudun hijira

- Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da nasarorin da rundunar sojoji ke yi a jihohi

- Ya shaida yadda suka samu nasarar yakar 'yan ta'addan da suka kawo musu hari a hanyar Maiduguri

- Ya kara da sanar da yadda suka samu nasarar kama wasu mutane 2 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Bauchi

Rundunar sojoji sun kashe fiye da 'yan ta'adda 3, yayin da suke kokarin kai wa tawagar masu mayar da 'yan gudun hijira zuwa garin Baga daga Maiduguri.

Kamar yadda kakakin rundunar, manjo janar John Enenche ya shaida, an kwaci miyagun makamai a hannunsu, bayan sun kama wani mai garkuwa da mutane a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba.

Enenche, ya bayyana hakan a hedkwatar tsaro da ke Abuja, yayin gabatar da jawabin sati a kan harkar tsaro.

Ya bayyana yadda suka kama wasu masu garkuwa da mutane, Yahaya Mohammed da Juli Ardo a kauyen Zalau da ke karamar hukumar Toro, da kauyen Lariki dake karamar hukumar Kirfi, duk a jihar Bauchi.

Ya ce yanzu haka wadanda ake zargin suna hannun hukumomin don fuskantar hukunci, Daily Trust.

Enenche ya bayyana cewa, rundunar Operation Wutar Tabki sun kai hare-hare ta sama, wadanda suka samu nasarar ragargazar maboyarsu a kauyen Ngosike, wani wuri da ke kusa da dajin Sambisa.

KU KARANTA: Hukumar Hisbah da KAROTA za su fara kama masu batsa wurin siyar da magungunan gargajiya

Dakarun soji sun kashe 'yan ta'adda, sun bankado harin tawagar 'yan gudun hijira
Dakarun soji sun kashe 'yan ta'adda, sun bankado harin tawagar 'yan gudun hijira. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro tace rundunar Operation Lafiya Dole ta ragargaji 'yan Boko Haram 13 tsakanin 22 ga watan Oktoba zuwa 29, Daily Nigerian ta wallafa.

Kakakin rundunar, John Enenche ya sanar da hakan ranar Juma'a, yayin da yake bayar da jawabi karshen mako a Abuja a kan arewa maso gabas.

Enenche ya ce sojojin rundunar OPLD na sama da kasa sun yi ayyuka da dama a cikin makonnan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel