Salamatu Abubakar: Mahaifiyar yara 3 da ke fentin mota a matsayin sana'a

Salamatu Abubakar: Mahaifiyar yara 3 da ke fentin mota a matsayin sana'a

- Wata mata 'yar Ghana wacce bata wuce shekara 35 da haihuwa ba, ta yi shekaru 20 tana aikin fentin mota

- Matar mai suna Salamatu Abubakari ta bayyana yadda rayuwa ta horar da ita har ta koyi sana'ar

- A cewarta, babban kalubalen da ta fuskanta shine yadda maza ke kawo mata tayin soyayyarsu daban-daban

Salamatu Abubakari wata mata ce 'yar Ghana mai yara 3, ta bayyana yadda tayi shekaru 20 tana aikin fentin mota.

Yanayin matar ya nuna bata wuce shekaru 35 ba a wata hira da Legit.ng suka yi da ita wacce gidan talabijin din SV suka nuna.

A cewarta, sana'ar ta kasance wacce maza suke yi, don haka ta fuskanci kalubale iri-iri, amma saboda dagewarta kwarewa a harkar, sai ta saba.

KU KARANTA: Mun shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma da tsakiya - Buhari

Salamatu ta bayyana yadda rayuwa tayi kunci bayan ta gama aji 3 na sakandare, kuma babu kudin da zata cigaba da karatu, don haka aka shawarce ta da ta fara sana'ar.

Salamatu Abubakar: Mahaifiyar yara 3 da ke fentin mota a matsayin sana'a
Salamatu Abubakar: Mahaifiyar yara 3 da ke fentin mota a matsayin sana'a. Hoto daga YouTube, SV TV Africa
Asali: UGC

Kamar yadda tace: "Da farko na tsani sana'ar saboda ni kadai ce macen da ta ke sana'ar kuma ina shan wahala.

"Amma bayan shekaru 20, ga yara 3, sana'ar ta bi jikina, har ina taimakon iyalina da ita."

A karshe, ta bayyana abinda yafi damunta, shine yadda samari da dama suke kawo mata tayin soyayyarsu.

KU KARANTA: Gadon sarauta: Rikici ya barke, an sace basaraken rikon kwarya tare da cin zarafinsa

A wani labari na daban, Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta fara kama masu magaungunan gargajiya da suke amfani da kalamen batsa wurin tallar magungunansu, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kirkiri wani kwamiti da ke karkashin kwamishinan lafiya, Dr Ibrahim Tsanyawa, KAROTA, Hisbah da sauran jami'an tsaro a matsayin 'yan kwamitin.

Sakataren ma'aikatar lafiyar jihar, Dr Usman Tijjani Aliyu, ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Laraba, inda yace an gama duk wasu shirye-shirye don fara ayyuka a kwamitin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel