EndSARS: Kwamitin bincike na jihar Legas sun ziyarci ma'adanar gawawwaki ta soji
- Bayan kafa kungiyar bincike da gwamnati tayi a kan kashe-kashen Lekki Toll Gate, a yau sun kai ziyarar ba zata
- 'Yan kungiyar sun samu shiga harabar asibitin sojoji da ke Ikeja, inda suka duba wurare daban-daban
- Sun tambayi inda kamarorin tsaro da sauran abubuwa suke, sai aka shaida musu cewa 'yan ta'addan sun konasu
Gwamnati ta kafa kungiyar bincike a kan kisan gillar da ake zargin sojoji sun yi wa masu zanga-zangar SARS da aka rushe, inda suka kai ziyara asibitin sojoji da ke Falomo, wurin Ikoyi a jihar Legas.
Da farko an hana masu binciken shiga harabar asibitin na tsawon mintuna 30.
Bayan an barsu sun shiga harabar, an kai su wurin da aka ce asibitin sojoji ne. Masu binciken sun shiga har bayan asibitin, wuraren wani kango.
A cewar ma'aikatan asibitin, dama ana gyara asibitin tun 2019, har yanzu ba'a karasa gyaran ba. Sun kai ziyarar ne don su yi bincike a kan kisan da ake zargin sojoji sun yi a Lekki Toll Gate.
Mai shari'a Doris Okwuobi, wacce ta wakilci matasa, ita ce ta jagoranci binciken, Rinu Odulala da Temitope Majekodunmi, suka tambayi jami'an da suka tsaya a Toll Gate din kamarar tsaro da sauran abubuwa da za su saukaka bincike.
Yayin zagayawa da masu binciken, shugaban Lekki Concession Company, Yomi Omomuwansu, yace bata-gari sun kona mafi yawan abubuwan.
Yau ne taro na biyu da suka yi tun bayan an zabi masu binciken a ranar 27 ga watan Oktoba.
KU KARANTA: Buhari ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya yayin Maulidi
KU KARANTA: Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London
A wani labari na daban, 'yan sanda sun samu nasarar damkar daya daga cikin fursinoni 1,993 da suka gudu daga gidan gyaran halin Oko da Benin, sakamakon kashe wani da yayi.
The Cable ta ruwaito yadda fursinoni suka gudu sakamakon rikicin zanga-zangar EndSARS.
Yayin da suka jera wadanda ake zargin masu laifi ne guda 126 a ranar Laraba, Babatunde Kokumo, kwamishinan 'yan sandan jihar, ya ce 10 daga cikinsu fursinoni ne da suka tsere.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng