Kuma dai, yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara, sun yi kashe rai

Kuma dai, yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara, sun yi kashe rai

- Bayan kwanak biyuda kisan mutane hudu a Garin Goga, yan bindiga sun sake kai hari Zamfara

- Wannan karon garin Dan Kurma suka far wa kuma suka kashe mutum daya

- Gwamna Matawalle ya bukaci shugaba Buhari ya dawo masa da jami'an SARS

Akalla mutane goma aka sace a garin Dan Kurma dake jihar Zamfara bayan kashe mutu daya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa daga cikin wadanda aka sace akwai matar maigari, Hajiya Baraka Sani Usman.

A cewar daya daga cikin masu idanuwan shaida, Malam Nasiru Habibu, ya bayyana cewa yan bindigan sun dira kauyen ne da safiyar Alhamis suna harbin kan mai uwa da wabi don tsoratar da mutane.

Habibu ya yi bayanin cewa yan bindigan sun shiga kauyen da manyan bindigu kirar AK47.

Ya kara da cewa mutan garin sun gudu daga muhallansu.

Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya tabbatar da aukuwa haka inda mutane 10 aka sace yayinda aka kashe mutum daya.

Shehu ya kara da cewa an tura jami'an yan sanda da Sojoji wajen domin kwantar da hankulan mutane.

KU KARANTA: Babu dan Najeriyan da zai ce ba'a samu canji ba - Ministan Lantarki

Kuma dai, yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara, sun yi kashe rai
Kuma dai, yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara, sun yi kashe rai Hoto: AsoVilla
Asali: Twitter

DUBA NAN: Ba yunwa ta sa ake satan kayan tallafin Korona ba, kwadayi ne kawai - Fadar shugaban kasa

Mun kawo muku rahoton cewa wasu yan bindiga a ranar Alhamis sun kai hari garin Gidan Goga dake karamar Maradun na jihar Zamfara, inda mutane akalla hudu suka rasa rayukansu.

Mazauna sun bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun dira garin kan babura suna harbin mutane kafin sukayi awon gaba da shanu da awaki.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai inda yace harin ya faru ranar Alhamis.

Wani tsohon kwamishanan ilimin jihar Zamfara, wanda dan gari Gidan Goga ne, Ibrahim Danmalikin Gidan Goga, ya bayyanawa Daily Trust cewa yan bindigan sun dira garin misalin karfe 1 na rana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel