An samu bindigu 65 a wurin masu laifi 157 da aka kama a Kaduna

An samu bindigu 65 a wurin masu laifi 157 da aka kama a Kaduna

- Jami'an 'yan sanda a jihohin Najeriya na cigaba da yin bajakolin batagarin matasa da aka kama bayan hargitsewar kasa a makonnin da suka gabata

- Batagarin matasa sun fake da zanga-zangar neman a kawo karshen rundunar SARS (ENDSARS) wajen barnatar da dukiyar gwamnati da daidaikun jama'a

- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta yi bajakolin mutane 157 da ta kama bisa zarginsu da aikata laifuka daban-daban

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta sanar da cewa ta kama mutane 157 da take zargi da aikata miyagun laifuka daban-daban.

Daga cikin mutanen 157 da aka kama akwai wadanda ake zargi da aikata fashi, satar shanu, fyade, garkuwa da mutane da kuma wadanda suka barnata kayan hukuma da na jama'a a jihar Kaduna.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, Umar Muri, ne ya bayyana hakan yayin holin wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar 'yan sandan jihar Kaduna a ranar Juma'a.

KARANTA: Barayi sun sace $2m daga kudin yakin neman zaben Trump a Amurka

Kazalika, ya bayyana cewa an samu bindigu 65, da suka hada da AK47 guda 24, a wurin mutanen da aka kama.

"A yau, ina mai murnar sanar da ku cewa a yunkurin rundunar 'yan sanda na sauke nauyin kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu da aka dora mata, mun samu nasarar kama 'yan ta'adda da batagari 157 a jihar Kaduna.

An samu bindigu 65 a wurin masu laifi 157 da aka kama a Kaduna
Wasu daga cikin masu laifi 157 da aka kama a Kaduna @tribune
Asali: Twitter

"Mutanen 157 da aka kama, a 'yan kwanakin baya bayan nan, sun aikata laifuka daban-daban da suka hada da; fashi da makami, fyade, satar shanu, kisa, garkuwa da mutane, barnatar da dukiyar gwamnati da sauran jama'a da kuma mambobin IMN da sauransu.

"Wasu daga cikin masu laifin sun bayar da muhimman bayanai a kan rawar da suka taka wajen aikata manyan laifuka, sun bayar da bayanan ne bisa zabinsu, ba tare da matsin lamba ba.

"Da zarar mun kammala bincike za mu tuntubi ma'aikatar Shari'a domin gurfanar da su a gaban kotu.

KARANTA: Zamfara: An yi batakashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga, ba a san adadin wadanda suka mutu ba

"A yayin da muke gudanar da bincike a kansu, mun samesu da kayan laifi daban-daban da suka hada da; bindigu AK47 guda 24, wasu manyan bindigu guda biyu, kananan bindigu guda uku, kananan bindigu da aka kera a gida guda 12, SMG biyu, bindigar baushe 16 da sauransu, wanda jimillarsu ta kama 65," a cewar kwamishinan.

Daga cikin sauran kayayyakin da kwamishinan ya lissafa cewa an samu a wurin mutanen da aka kama sun hada da; baburan hawa 23, Dalar Amurka $29,500 na bogi, N400,000 na bogi, buhunhunan kayan abinci da na taki da sauransu.

A ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa gwamnatin jihar Filato ta bayyana cewa muhimman wurare 22 mabarnata suka lalata a ta'adin da batagari suka tafka a Jos da Bukuru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel