Zulum ya bayyana matakin da zai dauka kan ɓata garin da aka yi haya don yin zanga zanga a Borno

Zulum ya bayyana matakin da zai dauka kan ɓata garin da aka yi haya don yin zanga zanga a Borno

- Gwamna Zulum ya ba zai zuba ido yana kallo wasu su kawo koma baya ga kokarin tabbatar da zaman lafiya a jiharsa ba

- Zulum ya umarci jami'an 'yan sanda da na DSS da su yi bincike kan wanda ke shirin daukar nauyin zanga zanga a jihar

- Gwamna ya shawarci masu ruwa da tsaki da su kyautata alaka da matasa da sauran bangarori don samun zaman lafiya da ci gaba

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya umarci 'yan sanda su tarwatsa duk wani mai zanga zangar da yayi kokarin taba zaman lafiyar jihar a cewar rahoton The Punch.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin taron masu ruwa da tsaki a Maiduguri a wani yunkurin gwamnatin tarayya na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Da yake jawabi, Zulum ya ce jihar Borno ta shiga wani yanayi mara dadi a baya bayan nan, ya kuma ce baza su zuba ido abin dake faruwa a wasu sassan kasar nan ya taba kokarin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya ba.

'Yan sanda zasu yi maganin duk ɓata garin da aka yi haya don yin zanga zanga - Zulum
Gwamnan Borno, Babagana Zulum. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Farautar 'yan bindiga suke yi' - Gwamnatin Kaduna ta yi karin haske kan jiragen sojoji da ke shawagi a jihar

"Tashe-tashen hankula a Borno ya samo asali ne daga wata zanga zanga da wasu wanda basa son yan sanda suka shiga, wanda hakan ya janyo fada tsakanin su da rundunar. Saboda haka, banga dalilin da zai sa wannan gwamnati ta bar irin wannan abin ya sake faruwa ba.

"Na samu rahoton cewa an dauki nauyin wasu bata gari da su fito su shirya zanga zangar kin jinin jami'an tsaro a Maiduguri. Na umarci yan sanda da DSS da su yi bincike, su gano su kuma gurfanar da duk wanda yake da a ciki komai matsayinsa," in ji gwamnan.

KU KARANTA: Hotuna: An kashe 'yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji - DHQ

Ya kuma yi kira ga sauran masu ruwa tsaki da su kyautata alaka da matasa da sauran bangarori don tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a jihar.

A wani labarin, gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa makiyan kasar nan suka lalata zanga zangar #endsars da nufin rushe kasar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata, 27 ga Oktoba a yayin tattaunawa da manema labarai kan yadda za a tabbatar da hadin kan Najeriya, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel