Bukin Maulud: Sauƙon Gwamna Obaseki ga Musulman Edo

Bukin Maulud: Sauƙon Gwamna Obaseki ga Musulman Edo

- Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya aika sakon Maulidi ga Musulman jihar

- Obaseki ya bukaci Musulman da su zamo masu aiki da koyarwar Annabi Muhammadu

- A yau Alhamis, 29 ga watan Oktoba ne al'umman Musulmi ke bikin zagayowar ranar haihuwar fiayyen halitta

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya taya al’umman Musulmi a jiharsa murnar zagaowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

Obaseki ya ja hankalin Musulman jihar a kan su ci gaba da koyi da kyawawan halayen manzon tsira.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a cikin jawabin maulidin Annabi da ya ke gudana a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba, jaridar Aminiya ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Bukin Maulud: Muhimman abubuwa 5 da Buhari ya faɗa wa yan Nigeria

Bukin Maulud: Sauƙon Gwamna Obaseki ga Musulman Edo
Bukin Maulud: Sauƙon Gwamna Obaseki ga Musulman Edo Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Obaseki ya ce, “Ina taya Musulmai maza da mata na jihar Edo da ma kasa baki daya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

“A wannan rana muna kira da Musulmai mu ci gaba da nuna kauna da zaman lafiya, domin cigaban jiharmu da kasa baki daya”, inji shi.

Ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da zama makwabta nagari kamar yadda yake a koyarwar Ma’aikin.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda wannan dan bautar kasar ya nemi auren kyakyawar budurwarsa bayan ya yi suman karya (bidiyo)

Daga karshe ya yi kiran samun hadin kan mutanen jihar domin wanzuwar zaman lafiya.

A gefe guda, yayin da musulman Najeriya ke farin cikin zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan Najeriya da su yi koyi da kyawawan halayen annabi Muhammadu (SAW).

Su nuna kauna da fahimta ga al'umma, da kuma bayyanar da kyawawan halayensa na hakuri, gaskiya, rikon amana da mutunci ga kowa, Premium Times.

A wani sako da shugaban kasa ya tura wa musulmai a kan maulidin fiyayyen halitta, wacce ta zama ranar hutu a Najeriya, ya roki 'yan Najeriya musamman matasa da su bar duk wani mummunan kudiri a kan zanga-zangar da ke jawo sace-sace da lalata dukiyoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel