Amina Mohammed, Bande da sauran wadanda Tauraruwarsu ta ke haskawa a waje
- Akwai wasu ‘Yan Najeriya da su ka samu manyan mukamai na Duniya
- Da dama daga cikinsu tsofaffin Ministoci ne da aka yi a gwamnatin kasar
- Wanda ake sa ran za ta zama sabuwar shiga a jerin ita ce Okonjo-Iweala
A cikin ‘yan shekarun bayan nan, an samu wasu mutanen Najeriya da ubangiji ya tsaga da rabonsu, su ka rike muhimman mukumai da ake ji da su a Duniya.
Wannan ruwan kujeru da aka yi wa ‘yan Najeriya ya zo ne a mulkin shugaba Muhammadu Buhari, wanda kasashen Duniya ke yi masa kallon dattijon kwarai.
Legit.ng Hausa ta kawo jerin wadannan zakakuran ‘yan Najeriya da su ke yin fice a waje.
KU KARANTA: Farfesa Tijjani Mohammed Bande ya samu kujera a UN
1. Amina J. Mohammed
Amina Mohammed mai shekaru kusan 60 ce mataimakiyar shugabar majalisar dinkin Duniya. Tsohuwar ministar ta hau wannan kujera ne a farkon 2017 bayan nada António Guterres.
Miss Mohammed ta ajiye kujerar Minista a Najeriya bayan ta samu wannan babbar kujera.
2. Tijjani Bande
A shekarar 2019 ne majalisar dinkin Duniya ta zabi wani mutumin Najeriya a matsayin shugaban zauren majalisa. Tijjani Bande ya sauka daga kan wannan kujera bayan shekara guda a 2020.
Farfesan ya fito ne daga jihar Kebbi, kafin nan shi ne wakilin Najeriya a majalisar dinkin Duniya.
KU KARANTA: Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin AfDB
3. Akinwumi Adesina
Wani mutumin Najeriya da ke cikin wannan jeri shi ne Dr. Akinwumi Adesina wanda ya taba rike kujerar ministan gona da raya karkaka a lokacin da D. Goodluck Jonathan ya ke mulkin kasar.
Akinwumi Adesina ya zama shugaban bankin cigaban Afrika har kuma ya samu ya zarce.
4. Ngozi Okonjo-Iweala
Rahotanni sun kuma nuna cewa babu mamaki Ngozi Okonjo-Iweala ta zama shugabar kungiyar WTO. Babu wata mace ko mutumiyar Afrika da ta taba rike wannan kujera a tarihinta.
A halin yanzu kusan duka kasashen kungiyar Turai da Afrika su na goyon bayan Okonjo-Iweala.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng