Yanzu Yanzu: Buhari ya gana da T.Y. Danjuma a fadar shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Buhari ya gana da T.Y. Danjuma a fadar shugaban kasa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga labule da T.Y. Danjuma

- Sun yi ganawar ne cikin sirri a fadar shugaban kasa da ke Abuja a yau Laraba, 28 ga watan Oktoba

- Zuwa yanzu ba a san takamaiman abunda za su tattauna a kai ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, ya yi ganawar sirri tare da tsohon ministan tsaro, Janar T. Y. Danjuma mai ritaya, a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Mista Sunday Aghaeze, mataimakin Shugaban kasa kan hotuna, ya tabbatar da hakan ta wani wallafan hoto kan ganawar.

Manema labaran fadar Shugaban kasa basu san manufar ganawar tasu ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Yanzu Yanzu: Buhari ya gana da T.Y. Danjuma a fadar shugaban kasa
Yanzu Yanzu: Buhari ya gana da T.Y. Danjuma a fadar shugaban kasa Hoto: Sunday Aghaeze
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Kowa yaci ya amayar: Ƴan sanda sun cafke mutane 238 da laifin satar kayan tallafi a Adamawa

Sai dai kuma an tattaro cewa ganawar tasu ba zai rasa nasaba da tattaunawar da ke gudana da manyan masu ruwa da tsaki a kasar ba domin neman mafita mai dorewa game da matsalolin tsaro da na tattalin arziki.

Shugaban kasar a ranar 23 ga watan Oktoba ya jagoranci wata ganawa mai muhimmanci tare da tsoffin shugabannin Najeriya ta yanar gizo a zauren fadar Shugaban kasa Abuja.

Dukkan tsofaffin shugaban Najeriya na Soja da Demokradiyya sun hallara ta yanar gizo yayinda hafsoshin tsaro da ministoci ke hallare a cikin fadar shugaban kasa.

Daga cikin tsofaffin shugabannin kasa da suka hhallara sune Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo, Abdulsalami Abubakar (Rtd), Goodluck Jonathan da Chief Ernest Shonekan.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya aike sakon ta’aziyya ga Ahmed Gumel ta mutuwar matarsa

Wadanda suka halarci ganawar sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; sakataren gwamnati, Boss Mustapha; Farfesa Ibrahim Gambari da NSA Babagana Monguno.

Sauran sune shugaban hafsoshin tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; IG na yan sanda, Mohammed Adamu; dirakta janar na DSS, Yusuf Bichi da diraktan NIA, Ahmed Rufa'i.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel