Sabon hari a Katsina: Yan bindiga sun sace mata uku yayin artabu da 'yan sanda

Sabon hari a Katsina: Yan bindiga sun sace mata uku yayin artabu da 'yan sanda

- Rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta samu nasarar dakile wani mummunan harin 'yan bindiga a karamar hukumar Safana

- Sai dai, a yayin musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da 'yan sandan, wasu 'yan bindigar sun sace mata uku, inda suka tsere tare da su zuwa cikin daji

- A hannu daya kuma, 'yan ta'addan sun harbe tare da kashe wani mutum mai suna Rabe Bala, mai shekaru 30, da ke zama a garin

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta samu nasarar dakile wani mummunan harin 'yan bindiga a garin Tsaskiya, karamar hukumar Safana.

A yayin da aka kashe 'yan bindiga biyar a nan take, sauran da suka tsere, sun samu nasarar sace mata uku tare da arcewa tare da su.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, a cikin wata sanarwa, ya ce an yi bata kashin ne bayan da suka samu rahoto mai karfi kan zuwan 'yan bindigar garin.

KARANTA WANNAN: Gwamnati ta lissafa muhimman wurare 22 da mabarnata suka lalata

Ya ce rundunar 'yan sanda tare da hadin guiwar sauran jami'an tsaro, sun yi nasarar dakile mummunan harin a garin Tsaskiya, tare da kashe biyar a cikinsu.

Gambo Isah ya ce "Akalla 'yan bindigar sun kai su 200 dauke da muggan makamai kirar GPMG da AK47, inda suka kutsa cikin garin, tare da fara harbin kan mai uwa da wabi.

Sabon hari a Katsina: Yan bindiga sun sace mata uku yayin artabu da 'yan sanda
Jami'an 'yan sanda
Asali: UGC

"Ana tsakiyar haka ne, jami'an tsaron suka farmaki kan 'yan bindigar, inda aka yi musayar wuta, lamarin da ya sa aka kashe biyar daga 'yan ta'addan, wasu kuma suka tsere da raunuka.

KARANTA WANNAN: DPO ya labarta yadda wasu fusatattun matasa suka so halaka shi a Kubwa

"A hannu daya kuma, 'yan ta'addan sun harbe tare da kashe wani mutum mai suna Rabe Bala, mai shekaru 30, da ke zama a garin.

"Haka zalika, 'yan bindigar yayin da suke barin garin, sun sace mata uku, inda suke tsere tare da su a cikin daji domin tsira da rayukansu."

Ya ce tuni rundunar ta tura jami'anta cikin dajin, domin bin sahun 'yan bindigar, domin kwato matan da kuma cafke wadanda aka jikkata ko gano gawar wadanda suka mutu a cikinsu.

A wani labarin, wasu masu garkuwa da mutane sun kashe SB Onifade, babban soja mai mukamin Kanal a rundunar sojin Najeriya.

Masu garkuwa da mutane sun kashe Kanal Onifade bayan karbar kudin fansa har Naira miliyan goma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel