Tsallake rijiya da baya: An kwaci babban Sarki da kyar bayan batagarin matasa sun kutsa kai fada

Tsallake rijiya da baya: An kwaci babban Sarki da kyar bayan batagarin matasa sun kutsa kai fada

- Har yanzu ana cigaba da samun sabbin rahotannin tafka ta'annati da mabarnata ke yi a sassan Nigeria

- Mabarnata na cigaba da kai farmaki wurare daban-daban mallakar gwamnati da daidaikun mutane

- Sai dai, harin da fustattun matasa suka kai fadar babban sarki, Akire na Ikire, a jihar Osun, bashi da nasaba da irin rahotannin barnar da ake cigaba da samu

A ranar Litinin ne wasu batagarin matasa suka kutsa kai tare da kai hari fadar Akire na Ikire, Sarki Olatunde Falabi, a jihar Osun.

Jaridar Punch ta rawaito cewa batagarin matasan sun ritsa Sarki Falabi a cikin fadarsa, inda suka tarfa shi, babu hanyar ficewa, kafin daga bisani wata tawagar jami'an tsaro ta zo ta kubutar da shi bayan tarwatsa matasan.

Shugaban karamar Irewole, Remilekun Abbas, ya dora alhakin faruwar abin a kan rigimar da ake yi a kan harkokin sarauta a masarautar Ikire.

KARANTA: Nigeria: Mabarnata sun haka fafakeken rami a titin da jirgin sama ke falfala gudu kafin ya tashi

"Abinda ya faru a Ikire bashi da nasaba da rikicin da ya balle sakamakon zanga-zangar ENDSARS. Rigima ce irin ta harkar nadin sarauta, ita ta haddasa tayar da wannan tarzoma.

Tsallake rijiya da baya: An kwaci babban Sarki da kyar bayan batagarin matasa sun kutsa kai fada
Mawaki Davido yana kwasar gaisuwa a gaban babban sarki a Kabilar Yoruba
Asali: Instagram

"Akwai gidan sarautar da ke rigima da dangin sarkin Ikire na yanzu, daga wancan gidan ne aka kitsa kawo wannan harin da aka kaiwa fadarsa.

"Ba a samu asarar rai ba. Jami'an tsaro sun kubutar da Sarki, sun daukeshi daga fadar. An baza Sojoji a tituna domin tabbatar da tsaro," a cewar Abbas.

KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar hutun bikin Mauludi

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Opolola ya ce sai da jami'an 'yan sanda suka kawo motarsu ta daukan makamai (APC) kafin su tarwatsa matasan da suka mamaye fadar, ba shiga, ba fita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel