Yanzu-yanzu: Bata gari sun kai hari sansanin NYSC na Abuja, suna wawan katifu

Yanzu-yanzu: Bata gari sun kai hari sansanin NYSC na Abuja, suna wawan katifu

- Yayinda matasa da suka kammala karatu ke shirin shiga sansaninsu, bata gari sun musu aika-aika

- Wasu matasa a unguwar Kubwa dake Abuja sun kai farmaki sansanin NYSC

- Sun debi kayayyakin abinci, katifu da wasu kaya masu amfani

Wasu bata garin matasa a ranar Talata, 27 ga Oktoba, sun fasa sansanin masu bautan kasa ta NYSC dake unguwar Kubwa, birnin tarayya Abuja.

Matasan sun wawashe katifu da wasu kayan alfanu.

KU KARANTA: Jerin kayayyakin da aka samu a gidan shugaban masu satar kaya a Calabar

Hakazalika a garin Madalla a jihar Neja ya nuna cewa, wasu daruruwan matasa sun kai mamaya wani dakin ajiya mai zaman kansa, mallakar wani dan Labanon a yankin.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa, matasa sun mamaye kamfanin wacce a baya aka sani da Madalla Floor Mill wanda ke a hanyar titin Abuja/Kaduna tun da misalin karfe 9:30 na safiyar yau Talata.

An tattaro cewa sun yi nasarar shiga kamfanin ta hanyar haura katanga.

An mayar da kamfanin Madalla Floor Mill zuwa dakin ajiyar kaya kwanakin baya inda yan kasuwa daga Suleja da sauran yankuna ke adana kayayyakinsu.

Yanzu-yanzu: Bata gari sun kai hari sansanin NYSC na Abuja, suna wawan katifu
Yanzu-yanzu: Bata gari sun kai hari sansanin NYSC na Abuja, suna wawan katifu
Asali: Original

DUBA NAN: Gwamnatin Saudiyya ta yi Alla-wadai da shugaban kasar Faransa

A wani labarin kuwa, shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya umarci kwamandojin rundunar soji da su dakatar da masu satar dukiyoyin gwamnati da na jama'a a cikin kasa.

Ya umarcesu da su yi gaggawar dakatar da duk wata baraka a kasar nan.

Daily Trust ta ruwaito yadda bata-gari suka yi ta amfani da damar zanga-zangar EndSARS wurin satar dukiyoyin al'umma, duk da kullen da aka yi ta sakawa a jihohin.

Sun cigaba da satar dukiyoyin gwamnati wadanda suka hada da kayan tallafin COVID-19, kayan shaguna, kasuwanni da sauran dukiyoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel