Lekki: Femi Falana ya ce sun fara bincike, sun nemo barikin sojojin da su ka yi harbe-harbe

Lekki: Femi Falana ya ce sun fara bincike, sun nemo barikin sojojin da su ka yi harbe-harbe

- Femi Falana ya tabbatar da Sojoji ne su ka harbi mutane a Lekki a ranar Talata

- Lauyan ya ce yanzu bincikensu ya gano barikin da aka dauko dakarun sojojin

- Ana ta nuku-nuku wajen bayyana ainihin wadanda su ka yi wannan danyen aiki

Femi Falana SAN, ya ce Alliance on Surviving COVID-19 And Beyond ta na binciken harbin masu zanga-zanga da aa yi a Lekki kwanakin baya.

Gawurtaccen Lauyan kuma ‘dan gwagwarmaya, wanda shi ne shugaban kungiyar ASCAB ya ce kawo yanzu sun gano barikin sojojin da su ka yi harbin.

Femi Falana ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Arise TV.

KU KARANTA: "Legas za ta bukaci Tiriliyan 1 a maida barnar da #EndSARS ta yi"

Falana ya hakikance a kan cewa sojoji ne su ka harbi masu zanga-zangar #EndSARS a ranar Talata, ya kuma ce har sun kai ga gano inda dakarun su ka fito.

Ya ce: “Mun riga mun gano barikin da sojojin da su ka zo Lekki su ka fito, mun bankado barikin.”

Amma a hirar da aka yi da shi a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, Lauyan bai kama sunan wani soja ko ya fadi sunan barikin da ya ke ikirari sun gano ba.

“Babu mamaki an sanar da shugaban kasa cewa an ba sojoji umarnin yin haka, shiyasa aka ki duba lamarin. Rade-radi ne, amma bayanai sun fara fitowa.” Inji sa.

KU KARANTA: Mufti Menk da Fafaroma sun yi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya

Lekki: Femi Falana ya ce sun fara bincike, sun nemo barikin sojojin da su ka yi harbe-harbe
Femi Falana Hoto: politicsnigeria.com
Asali: UGC

Falana ya ce: “Shakka babu sojoji sun je Lekki, hakika sun harbi masu zanga-zanga, akalla daga ciki biyu sun mutu a dalilin raunin da harbin bindiga ya yi masu.”

Lauyan da ake ji da shi ya ce gwamnatin Najeriya ba ta san doka ba. “Gwamnati ta killace duk wani wurin zanga-zanga, saboda a hana fita ayi zanga-zanga.”

A ranar Litinin ne gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana wadanda suka yi harbe-harbe a Lekki, bayaninsa ya gaskata abin da Femi Falana ya fada.

Babajide Sanwo-Olu ya ce bidiyon da suka samu ya nuna cewa sojoji ne suka harbi Bayin Allah.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel