Dalilin da yasa muka bar jama'a suka kwashe tallafin korona - Dan sanda

Dalilin da yasa muka bar jama'a suka kwashe tallafin korona - Dan sanda

- Tunda zanga-zangar EndSARS ta canja salo ta koma sace-sace da kone-konen dukiyoyin gwamnati da na al'umma, 'yan sanda sun zura ido suna kallo

- Mutane da dama sun yi ta mamakin yadda jami'an suka zurawa sarautar Allah ido basa daukar wani mataki a kan wannan barakar a jihohi

- Wani jami'in 'yan sanda, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana hujjoji kwarara wadanda suka sa jami'an suka dauki wannan matakin

Sace-sace da matasa ke ta yi sun cigaba da faruwa a ma'ajiyar gwamnati, inda suke sace kayan tallafin COVID-19 wadanda ya kamata a raba tun lokacin da gwamnati ta saka kulle.

Duba da faruwar wannan lamarin ne 'yan sanda suka zura idanu suna kallo ana sata basu daukar wani mataki a kai, Daily Trust.

Wani 'Dan sanda da ya bukaci a sakaya sunansa ya yi magana a kan zura idon da 'yan sandan suka yi a kan al'amarin a matsayinsa na jami'in tsaro.

Kamar yadda aka yi hira da shi, inda aka tambayeshi dalilin zurawa masu zanga-zangar ido suna ta bankawa kayan gwamnati wuta bayan sace wasu.

Cewa yayi: "Kun san cewa 'yan ta'adda sun tsani ganin 'yan sanda, kuskuren 'yan sanda na farko shine rushe rundunar SARS, saboda a watannin karshen shekara ba'a rushe kungiya mai yaki da ta'addanci irin SARS.

"Kamata yayi a tabbatar an yi bincike Mai tsanani a kan lamarin, sai ayi kokarin yin gyara a kan barakar da aka samu.

"Na biyu, kamata yayi ace a Najeriya ana yin horo mai tsanani ga jami'an 'yan sanda, tun daga kan kwamishina har kasa, domin wasu jami'an ba su san hakkokin jama'a ba balle har su karesu.

"Ta ya za'ayi ace wanda aka hora yayin shiga aikin 'yan sanda tun shekaru 15 zuwa 20 su san sababbin tsarin da kasa ta tanadar a shekarunnan?"

KU KARANTA: Wawushe dukiyoyin jama'a : 'Yan sanda sun damke mutum 224 a jihohi Kwara da Cross River

Dalilin da yasa muka bar jama'a suka kwashe tallafin korona - Dan sanda
Dalilin da yasa muka bar jama'a suka kwashe tallafin korona - Dan . Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Harbin Lekki: Buhari ya magantu, ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya

A wani labari na daban, rahotanni sun nuna yadda bata-gari suka saci dukiyoyin gwamnati, ciki har da kayan abincin tallafin COVID-19 a ranar Asabar. An umarci bata-garin wadanda suka yi satar da sunan zanga-zangar EndSARS da su mayar da duk abubuwan da suka sata cikin kwana 3.

Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, yayin da yake zagaye jihar don ganin barnar da suka yi a jiharsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel