Sadiya Farouq ta kara farin jini a sakamakon gano kayan tallafin da aka adana
- Ministar bada agaji ta kasa ta kara samun farin jini a cikin ‘yan kwanakin nan
- A baya an rika sukar Sadiya Farouk da ta ce gwamnatinsu ta raba kayan tallafi
- Yanzu mutane su na ganin wadannan kaya da ta raba, amma jami’a su ka boye
Gano kayan tallafin annobar COVID-19 da aka boye a jihohin Najeriya, ya tabbatar da cewa da gaske gwamnatin tarayya ta yi nufin a taimaki Bayin Allah.
Kafin yanzu, an yi ta sukar Ministar bada agajin gaggawa, Sadiya Umar Farouq, ana yi mata kallon mai labaran kanzon kurege a duk lokacin da ta yi magana.
Babu shakka yanzu an wanke Ministar, haka-zalika ra’ayoyin mutane game da ita ya canza kamar yadda tattaunawar da ake yi a kafafen zamani su ka nuna.
Jaridar Daily Trust ta tattaro wasu daga cikin abin da jama’a su ke fada a Twitter kamar haka:
KU KARANTA: Tinubu: Na san za ayi mani barna a wajen zanga-zanga, amma na yi gum
Wani ya ce: "Sadiya Umar Faruq ba karya ta ke yi ba lokacin da ta ce ta raba kayan tallafi. Wasu jami’an gwamnati ne su ka boye a dakunan adanarsu. Masu bore ne su ka tabbatar da gaskiyarta. Hajia a gaida ango... Allah ya saka da alheri!"
— OG_shabab Tha_WeedLord (@GrassLord_) October 25, 2020
Nabeela Ahmadu ta rubuta: "Sadiya Umar Faruq ta ce ta raba kaya na biliyoyi ga kowace jiha, amma aka yi mata tabon karya, aka kira ta da sunayen cin mutunci."
— Mrs. Nabeela Ahmadu (@AhmaduNabeela) October 24, 2020
Ita kuwa Aisha Bukar cewa ta yi: “Mama ki yi hakuri ki yafe mana, mun zarge ki da wawure kayan tallafin COVID-19.”
— Aesha bukar (@Aesha_bukar) October 25, 2020
"Abin takaici, ba mu yarda da ita ba. Wadanda aka ba alhakin raba kayan su ka jawo wannan, su ka sa aka rika yi mata kallon makaryaciya." Inji wani matashi."
— YOUTH DEMOCRATIC PARTY (YDP)✊ (@TobiPaul13) October 24, 2020
KU KARANTA: Fafaroma ya fito ya roki al’umma su sa mutanen Najeriya a addu’a

Asali: UGC
Amma wasu sun ce kayan abincin da ake yin awon-gaba da su ba wadanda gwamnati ta raba ba ne, attajirai ne su ka bada gudumuwar kayan tallafin Ca-COVID.
"Kayan Ca-COVID-19 dabam da na gwamnatin tarayya. Dole (Minista) ta amsa tambaya game da yadda aka raba abinci ga ‘yan makaranta yayin da su ke gidajen iyayensu." Inji wani.
— MESCANA™ (@realmetrah) October 24, 2020
Chiefa Ababiaka ya ce: “Yau mun gani cewa gwamnoninmu mugaye ne, kuma su na cikin matsalolinmu.”
— Lagos Landord and 36 Tenants GCFR (@chiefagbabiaka_) October 24, 2020
"Ku kuma gwamnoninmu, akwai Allah." Inji Babagana Shettima.
— Babagana Shettima (@Shettima009) October 24, 2020
A Bauchi, mutane sun je wawurar tallafin COVID-19, amma su ka sha kunya domin kuwa sun makara, sun ga cewa Gwamna ya gama rabon kayan tuni.
Bala Mohammed ya ce abin da ya sa Jama’a ba su samu komai ba shi ne ya ba mabukata kayan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng