Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar ta baci a kananan hukumomi 21
- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya kakaba dokar ta baci ta tsawon 24 a dukkan kananan hukumomin jihar
- An saka dokar takaita zirga-zirga a fadin jihar Kaduna ne biyo bayan barnatar da kayan tallafin korona da batagarin matasa ke yi a sassan Najeriya
- Mista Samuel Aruwa, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na Kaduna, ya sanar da sassauta dokar ta bacin a kananan hukumomi 21
Gwanatin jihar kaduna ta karbi shawarar hukumomin tsaro na sassauta dokar ta baci a kananan hukumomin jihar guda 21.
Sai dai, dokar ta baci ta tsawon 24 za ta cigaba a kananan hukumomin Chikun da Kaduna ta kudu har zuwa sanarwa ta gaba da za a fitar ranar Talata, kamar yadda kwamishinan tsaron cikin gida na Kaduna, Mista Samuel Aruwan, ya sanar.
A cikin sanarwar, Mista Aruwan ya bayyana cewa; ''jama'a zasu iya fita harkokinsu na yau da kullum daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 4:00 na yammacin kowacce rana daga ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, a kananan hukumomi 21.
"Dokar ta baci ta tsawon sa'a 24 tana nan daram a kanan hukumomin Chikun da Kaduna ta kudu".
DUBA WANNAN: An kashe jami'in kwastam a jihar Jigawa, an gudu da bindigarsa
Mista Aruwan ya kara da cewa ana shawartar mazauna kananan hukumomin biyu su cigaba da zama a gida har zuwa sanarwa da gaba da zata fito ranar Talata.

Asali: Twitter
A baya Legit.ng ta wallafa cewa hukumar kula da kafafen watsa labarai na kasa (NBC) ta ci tarar gidan talabijin din AIT, Channels 24, da 'ARISE Television saboda nuna rashin kwarewa yayin yada rahotannin zanga-zangar ENDSARS.
Armstrong Idachaba, mukaddashin babban darektan NBC, ne ya sanar da hakan yayin taron da ya yi da manema labarai ranar Litinin a Abuja.
DUBA WANNAN: Tallafin korona: Bidiyon matasa suna balle ma'adanar kayan abinci a Yola
An ci tarar manyan gidajen talabijin din uku miliyan tara kowannensu bayan zarginsu da yada wasu hotuna da bidiyon zanga-zanga da 'ba a tantancesu ba'.
NBC ta dade da gargadin kafafen yada labarai da ke Najeriya a kan su yi taka tsan-tsan da irin rahotannin da zasu yada yayin zanga-zanga domin gudun tunzura jama'a da kuma kunyata hukuma da sauran jama'a.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng