Wawushe dukiyoyin jama'a : 'Yan sanda sun damke mutum 224 a jihohi Kwara da Cross River

Wawushe dukiyoyin jama'a : 'Yan sanda sun damke mutum 224 a jihohi Kwara da Cross River

- Rundunar 'yan sandan jihar Kwara da ta Cross River sun cafke mutum 244 a kan zarginsu da sata

- Jama'ar suna daga cikin matasan da suka saci kayan gwamnati da na jama'a a yayin zanga-zangar EndSARS

- Kamar yadda kwamishinonin 'yan sandan jihohin suka sanar, an kama wadanda ake zargin da kayan satan

Rundunar 'yan sandan jihar Kwara a ranar Litinin ta tabbatar da kamen mutum 144 da ke da alaka da satar kayan gwamnati da na jama'a a Ilorin da ke jihar Kwara.

Bata-gari da suka boye karkashin inuwar masu zanga-zangar EndSARS a Ilorin a ranar sun dinga satar kayayyakin shaguna da na ma'aikatu. Sun dinga cin zarafin masu ababen hawa da kuma mazauna birnin.

A yayin zantawa da manema labarai, kwamishinan 'yan sandan jihar, Kayode Edbetokun, ya ce sun yi kamen ne bayan kokarin jami'an tsaro na hadin guiwa a jihar, The Nation ta wallafa.

Hakazalika, rundunar 'yan sandan jihar Cross River ta cafke wasu bata-gari 80 da ake zargi da hannu a cikin lalata kayan gwamnati a tsakanin 23 ga watan Oktoba zuwa 24 ga wata a Calabar.

Hukumar ta ce wadanda aka kama sun hada da wadanda suka shiga gidaje da ofisoshin 'yan majalisu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa an ga masu satar suna kwashe adaidaita sahu da babura.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Abdulkadir Jimoh, wanda ya zanta da manema labarai a ranar Litinina Calabar ya ce 'yan sanda sun samo kayayyakin satan, The Nation ta wallafa.

KU KARANTA: Hare-haren Legas shiryayyu ne, yunkurin durkusar da tattalin arziki ne - Gwamnonin Kudu

Wawushe dukiyoyin jama'a : 'Yan sanda sun damke mutum 224 a jihohi Kwara da Cross River
Wawushe dukiyoyin jama'a : 'Yan sanda sun damke mutum 224 a jihohi Kwara da Cross River. Hoto daga @Dailytrust
Asali: UGC

KU KARANTA: Harbin Lekki: Buhari ya magantu, ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kori hadimansa na musamman da ke bashi shawara a kan tsaro da wasu jami'ai uku a kan kone ofisoshin 'yan sanda da wasu kadarorin gwamnati a jihar.

A wata takardar da ta fito daga sakataren gwamnatin, Kenneth Ugbala, a ranar Lahadi, ya ce mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai, Nchekwube Aniakor da wasu shugabanni uku, ya sallamesu.

Shugabannin da aka sallama sun hada da Amos Ogbonnaya, Jerry Okorie Ude da Martha Nwankwo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng