Bidiyon yadda matasa suka fasa rumbun ajiyan tallafin korona a Gwagwalada, Abuja
- Wasu matasa da ke yawon neman rumbun ajiya sun balle ma'adanar kayayyakin tallafin korona a yankin Gwagwalada, Abuja
- Sun saci kayayyaki irin su shinkafa, semovita, taliya, siga, gishiri da taki
- Lamarin na zuwa ne yayinda sassa daban daban na kasar ke ci gaba da fuskantar hare-haren bata gari
Jama’a da ke yawon neman wajen da aka ajiye kayan tallafin korona sun kai farmaki wani rumbun ajiye kaya a Gwagwalada, babbar birnin tarayya, Abuja.
Kayayyakin da suka sace sun hada da shinkafa, semovita, taliya, siga, gishiri da taki.
Rumbun ajiyar wanda ke kusa da ofishin WAEC, an tattaro cewa yana dauke da kayayyaki mallakar hukumar birnin tarayya.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buratai ya shiga labule da manyan kwamandojin rundunar soji kan zanga-zangar EndSARS
A ranar Lahadi ma wasu matasa sun fasa wani rumbun ajiya a yankin Jabi kuda da kotun kula da da’ar ma’aikata.
Ba tare da duba kasancewar sojoji da yan sanda a wajen ba, matasan sun yashe kayayyaki daban-daban da aka ajiye a rumbun.
Ga bidiyon a kasa kamar yadda Channels Television ta wallafa:
A wani labarin kuma, Mazauna jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya sun fasa ma'adanar kayan tallafin COVID-19 da aka bai wa jihar.
Kamar kowacce jihar, sun kwashi iyakar kayan da za su iya kwasa sannan suka yi awon gaba da su, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Balle wuraren adana tallafin korona a jihohi ya fara daga yankin kudancin kasar nan bayan zanga-zangar EndSARS.
KU KARANTA KUMA: An kashe mutum 1 yayinda bata gari suka yi yunkurin kona ofishin yan sanda a Ibadan
Lamarin ya cigaba da shigowa jihohin arewa inda fusatattun matasa ke nemo ma'adanar kayan rage radadin.
Sakamakon yawaita balle ma'adanar kayayyakin tallafin, gwamnatocin jihohi daban-daban sun saka dokar ta-baci.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng