Garin daɗi na nesa: Gwamna Zulum ya rabawa zawarawa N65m a garin Rann

Garin daɗi na nesa: Gwamna Zulum ya rabawa zawarawa N65m a garin Rann

- Gwamna Babagana Zulum ya ziyarci garin Rann da ke karamar hukumar Kala-Balge ta jihar Borno

- Zulum ya rarraba kudaden tallafi ga mabukata da suka rasa iyalansu don su samu damar amfani da kudaden wajen siyan kayayyakin amfani

- Ya ba akalla magidanta 8,000 tallafi, inda kowanensu ya mika musu kudaden hannu da hannu

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Asabar, ya raba naira miliyan 65 a Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala-Balge da ke jihar.

Wannan shine karo na biyar da Zulum ke irin wannan tafiya na bayar da tallafi a Kala-Balge tun bayan da ya karbi mulki a watan Mayun 2019.

Rann mai makwabtaka da kasar Kamaru, sun gamu da ibtila’in ambaliyar ruwa daga babbar madatsar ruwa da ke Afrika ta Tsakiya, lamarin da ya tilasta musu hijira zuwa kasar ta Kamaru domin neman mafaka.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga

Mafi akasarin lokuta, mazauna kauyukan kan siyi kayan abinci daga kauyukan da ke iyaka a Jumhuriyyar Kamaru, jaridar The Nation ta ruwaito.

Zulum, a tafiyar ranar Asabar, ya kula da rabon kudin naira miliyan 65 ga zaurawa 8,000 da wasu marasa gata a garin Rann domin su samu damar siyan abinci da sauran kayan amfani daga kauyen iyakar Kamaru.

Garin daɗi na nesa: Gwamna Zulum ya rabawa zawarawa N65m a garin Rann
Garin daɗi na nesa: Gwamna Zulum ya rabawa zawarawa N65m a garin Rann Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

An ba kowani gida tsakanin 5,000 da 10,000 saboda babu tsarin banki a garin Rann.

Maza 5,000 sun samu 10,000 kowannensu da shinkafa buhun 10kg.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar hana fita ta awanni 24

Zulum, a watannin Yuni da Disamban 2019, ya kai wa al’ummar Rann ziyara, sannan ya sake kai ziyara yankin a cikin watannin Fabrairu da Yunin 2020.

A dukkanin ziyarar, gwamnan ya kula da rabon kayan abinci da sauran kayan tallafi.

Kafin tafiya Kala-Balge, Zulum ya kasance a Kaduna a ranar Juma’a wajen taron gwamnonin arewa.

Ya yi amfani da damar wajen duba kayayyakin jihar da ke Kaduna, ciki harda masaukin Kaduna da fadar Shehun Borno, masaukin gwamnati da ofishin jami’in hulda, kwatas din ma’aikatan gwamnati da otel din Borno.

A wani labari na daban, Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bada labarin yadda ta kaya tsakanin matasan jihar da shugaban ma’aikatan fadarsa, Ladan Salihu.

Wasu miyagu sun zo dakin adana na jihar Bauchi su na neman awon gaba da kayan tallafin COVID-19, amma ba su tashi da ko allura ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel